Home / Labarai / Gwamna Dikko Umaru Radda  Ya Amince Da Nadin Malam Nura Tela A Matsayin Sabon Akanta Janar 

Gwamna Dikko Umaru Radda  Ya Amince Da Nadin Malam Nura Tela A Matsayin Sabon Akanta Janar 

Daga Imrana Abdullahi

Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar ta ce

Malam Nura Tela ya fito daga Jikamshi da ke karamar hukumar Musawa a jihar Katsina.

Nadin sabon Akanta Janar din a cewar Mohammed Kaula, ya biyo bayan kwazonsa da kwarewarsa ne ta hanyar aikin da ya yi a baya a matsayin mai taimaka wa gwamna, tare da mayar da hankali musamman kan harkokin Baitulmali.

Mohammed Kaula ya ce nadin nasa a hukumance zai fara aiki ne daga ranar 31 ga Agusta, 2023.

Malam Nura Tela zai karbi mukamin ne daga hannun Alhaji Malik Anas, wanda ya yi aikin a  jihar na tsawon shekaru 35 a matsayin Akanta Janar mai barin gado, wanda ya yi ritaya daga aikin gwamnati a ranar 30 ga Agusta, 2023.

“Alhaji Malik Anas a sabon mukaminsa na mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin banki da kudi, ya jajirce wajen daukaka darajar kudin jihar,” Ibrahim Kaula Mohammed ya jaddada hakan.

Ya lura cewa, an tsara naɗin ne don ƙarfafa jagoranci na kuɗi, dabaru da kuma samar da kyakkyawan manufofi na alkairi.

Ibrahim Kaula Mohammed ya bayyana cewa, duk mutanen biyun Malam Nura Tela da Alhaji Malik Anas za su fara aiki a hukumance a ranar 31 ga Agusta, 2023.

Mohammed Kaula ya tabbatar da cewa “Ofishin gwamna yana da kwarin guiwa kan iyawarsu na bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban jihar.”

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.