Home / Labarai / Daukar Jami’an KADVS Dubu 7,000 Zai Taimakawa Wajen Inganta Tsaro A Jihar Kaduna 

Daukar Jami’an KADVS Dubu 7,000 Zai Taimakawa Wajen Inganta Tsaro A Jihar Kaduna 

Daga Imrana Abdullahi

Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana cewa daukar mutane dubu Bakwai zai taimakawa inganta harkokin tsaro a Jihar Kaduna.

Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen kaddamar da fara bayar da horo ga mutane 7,000 da aka zabo su daga kananan hukumomin Jihar baki daya.

An dai kaddamar da bayar da horon ne a kwalejin horar da jami’an Yan Sanda da ke Kaduna.

Jami’an tsaron da suke karkashin KADVS tun da aka kafa su a Jihar Kaduna sun kasance masu aiki tukuru wajen bayar da gudunmawa domin samar da nasarar tsaron dukiya da lafiyar jama’a.

Kuma hakan na nuni ne da irin yadda wannan Gwamnatin ke kokarin cika alkawarin da aka yi wa jama’a tun lokacin fafutukar neman zabe. Kuma muna tabbatarwa da jama’a cewa Gwamnati na sane da irin kokari da gudunmawar da Jami’an KSDVS Duke bayarwa domin sun kasance suna aiki tare da dukkan hukumomin tsaro a Jihar Kaduna da nufin yin maganin matsalar masu aika aika da ke baranar ga tsaro.

Karanci masu aikin tsaro na yin barazana wajen yaki da yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka duk sakamakon irin wadannan abubuwan ne yasa a halin yanzu Gwamnati ta yanke shawarar daukar karin mutane dubu 7,000 da za su yi aikin sa idanu da tara bayanai ta KSDVS.

GWAMNA UBA Sani ya ci gaba da bayanin cewa aikin jami’an wannan hukuma ta KADVS shi me taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri da nufin magance matsalar tsaro

Sai ya yi kira ga jami’an da za a ba su horo a kwalejin horar da jami’an yan Sanda ta Kaduna da su gujewa duk wani kokari na take hakkin jama’a kuma su tsaya a kan tsari da tanajin da KADVS keda shi a wajen duk aiwatar da aiki.

Gwamna Uba Sani kenan lokacin da yake gaisawa da wadanda za a ba horon

Gwamna Uba Sani ya kuma mika godiyarsa ta musamman ga shugabannin al’umma da malaman addini, shugabannin kananan hukumomi, kwamishinan Yan Sanda, Daraktan rundunar taaron DSS, Kwamandan kwalejin horar da Yan Sanda da ke Kaduna da dukkan shugabannin hukumomin tsaro bisa irin yadda suke taimakawa ga jami’an KADVS haka kuma muna godiya kwarai ga shugaban KADVS

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.