Home / News / Gwamna El-Rufa’i Ne Ya Dace Ya Gaji Buhari – Dakta Yahya Sale
Tambarin Mujallar Garkuwa kenan
Tambarin Mujallar Garkuwar Jama'a

Gwamna El-Rufa’i Ne Ya Dace Ya Gaji Buhari – Dakta Yahya Sale

DARAKTAN Tsangayar Kula da muhalli da makamashi ta Jami’ar Jihar Kaduna, Dokta Yahya Saleh Ibrahim Kayarda ya bayyana cewa a duk gwamnonin Najeriya, babu wanda ya kamata ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari, a zaben shugaban kasa mai zuwa na shekara ta 2023, kamar Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i. Dokta Yahya Saleh Ibrahim Kayarda, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce a duk gwamnonin Najeriya  babu wanda ya kai Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i aiki, kuma shi ne wanda tun da ya hau kan mulki, har ya zuwa wannan lokaci yake tare da shugaban kasa Buhari. Don haka babu wanda ya kamata ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na shekara ta 2023 kamar Malam Nasiru El-Rufa’i.

 Ya ce  Nasiru El-Rufa’i  baya tsoron ya yi abin da zai taimaka wa talaka kuma ba ya tsoran ya aikata, abin da zai kare mutumcin Najeriya. Kuma  baya tsoron ya rasa rayuwarsa wajen kare rayuwar talakawan da yake mulka. Domin kowa ya ga yadda yake bin barayi, ba tare da wani tsoro ba.

Ya ce  shi kadai ne Gwamnan da ya fito ya gaya wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kurakuransa. Domin  shi ba ya tsoran ya fadi gaskiya, ko ya aikata gaskiya. Kuma shi kadai ne dan siyasar da ba shi da ubangida a cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya.

Dokta Yahya Saleh ya yi bayanin cewa gwamna Nasiru El-Rufa’i ne ya fara aiki da sabon tsarin albashin ma’aikata na kashi 30 a cikin gwamnonin Najeriya. Sannan kuma ya yi ayyukan da dama na bunkasa harkokin ilmi da samar da hanyoyi a Jihar Kaduna.

Ya yi kira ga al’ummar Najeriya  su fito su zabi wanda ya cancanta, a zaben shugaban kasa na shekara ta 2023, ba tare da la’akari da jam’iyya ko addini ko bangaranci ba.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.