Home / News / Gwamna Ganduje Ya Dakatar Da Salihu Tanko Yakasai

Gwamna Ganduje Ya Dakatar Da Salihu Tanko Yakasai

Gwamna Ganduje Ya Dakatar Da Salihu Tanko Yakasai
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya Dakatar da mai bashi shawara a kan kafofin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai saboda abin da ya rubuta a kafar Sada zumunta a game da shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari.
Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Kwamared  Muhammad Garba, wanda ya isar da sakon umarnin Gwamnan a wata sanarwa a ranar Lahadi ya ce dakatarwar za ta fara aiki ne nan take.
Ya ce duk da yake mai taimakawar a kan batun kafafen yada labarai ya bayyana batun a matsayin wani tunani da ra ayinsa na kashin kansa, amma a matsayin wanda ke yin aiki tare da Gwamnati, zai yi wahala a bambance tsakanin ra’ayinsa da kuma na musamman daga Gwamnati da ya shafi aiyuka irin na hukuma.
Gwamnan ya kuma ja kunnen masu rike da mukamai na siyasa da aka nada su da masu aikin Gwamnati da su gujewa yin duk wani furicin da zai haifar da tashin hankali da kuma dumama al’amuran siyasa.
Takardar ta kuma yi bayanin cewa Gwamna Ganduje zai ci gaba da bin tsare tsare da shirye shiryen Gwamnatin Muhammadu Buhari.

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.