Home / Big News / Gwamna Masari Ya Tabbatar Da Mutuwar Likitan Da Ya Kamu Da Korona A Katsina

Gwamna Masari Ya Tabbatar Da Mutuwar Likitan Da Ya Kamu Da Korona A Katsina

Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya tabbatar da mutuwar Dakta Aliyu Yakubu, likitan da ya kamu da cutar Korona bairus da ke aikin Likitancin a garin Daira.
Ya bayyana wa manema labarai cewa hakika likitan da ya kamu da wannan kwayar cuta ta Korona Bairus mai suna Dakta Aliyu Yakubu da yake aikin likitanci a a Daura ya mutu.
 Masari ya shaidawa manema labarai hakan ne inda ya tabbatar masu cewa Dakta Aliyu Yakubu da yake aiki a asibiti mai zaman kansa da ya yi tafiya zuwa Legas kwanan nan, wanda da ya dawo ya kai kansa babban asibitin sojojin sama da ke Daura, awoyi biyu bayan nan ya mutu.
Ya ce an kuma dauki jininsa zuwa wurin Gwajin cutar Korona Bairus da ke Abuja inda aka tabbatar yana dauke da cutar babu ko tantama, yana da Covid 19 da hawan Jini da kuma Haifataitus duk baki daya.
Gwamna Masari ya kuma tabbatar da cewa tuni aka bayar da umarnin a lalubo dukkan mutanen da marigayin ya yi mu’amalla da su domin a yi masu Gwaji a kodai Abuja ko Legas.
Gwamnan ya kashi takobin ganin a baki dayan Jihar an ci gaba da daukar matakan kariya da kuma yaki da cutar Korona bairus da ake kira Covid – 19.
Kamar dai yadda bayani daga majiya mai tushe ta kyankyasa mana cewa Likitan dan asalin wata Jiha ne da yake aiki a asibitin mai zaman kansa, da idan hali ya yi zaku ji bayanai sosai.

About andiya

Check Also

APC RELOCATES TO NEW STATE HEADQUARTERS IN GUSAU, ZAMFARA

The Zamfara State chapter of the All Progressives Congress APC has today relocated to its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.