Home / Idon Mikiya / Gwamna Muhammad Badaru Ya Taimakawa Mata – Yalwa

Gwamna Muhammad Badaru Ya Taimakawa Mata – Yalwa

Kwamishiniyar ma’aikatar kula da harkokin Mata ta Jihar Jigawa Hajiya Yalwa Dabo Tijjani, ta bayyana wa manema labarai a kaduna irin nasarorin da aka samu a Jihar a bangaren kula da harkokin mata karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ga yadda tattaunawar ta kasance a hirar da suka yi da wakilinmu Mustapha Imrana Abdullahi.
Garkuwa: Gashi kun halarci babban taron horaswa na kwanaki biyu a Jihar Kaduna
Kwamishina: Hakika wannan babban taron horaswa da muka halarta na kwanaki biyu a kaduna mun karu da abubuwa da dama da aka sanar damu da kuma wadansu mun Sani amma kuma an kara mana haske kwarai game da ci gaban da aka samu, don haka muna kokarin nemawa mata yancinsu a koda yaushe duk inda ya kamata ayi hakan zamu nema masu yanzu.
Gwamnan Jigawa Gwamna ne na adalci kuma Gwamnan mu ne na mata, Saboda koda ya hau mulki a farko ma ya fara cikawa mata alkawarin da ya yi masu saboda haka duk abin da ya kasance ci gaban mata ne ba abin da zai hana shi yi.
Kuma wannan bitar karin dan ba ce a kan abin da zamu nuna wa mata.
Garkuwa: Kamar wadanne irin abubuwa ne Gwamnan Jihar Jigawa ya yi domin ci gaban mata?
Kwamishina: To Alhamdulillah abin da dai ya fara yi mana lokacin da ya hau mulki na farko ya fara ne da bayar da kiwon Awakai, Alhamdulillahi a lokacin ana yi masa zambo ana ce masa Gwamna mai Awaki da sauran meye da waye amma sai ga wasu jihohin ma suna zuwa Jigawa suna yin koyi da abin da aka yi na ba mata kiwon Awaki da ya zuwa yanzu mun ba mata dubu 42,123 min ba su Awakin nan kuma yanzu mun fara yin zagaye na biyu da mace Ashirin daga kowace mazaba.
Alhamdulillahi 20 din nan da muka fara na farko wata Goma 18 dinsu ya cika kuma tuni an karbi Awakin daga wasu matan an ba wasu kuma.
An kuma karba ne an ba kodai yar mutum ko kani ko magwabta sai a ba wasu domin ba a karba a fita da su a kai su wani wuri, kuma zagaye na biyu da muka fara shi ne ana ba mata Arba’in Arba’in a kowace mazaba.
Kuma bayan mun yi wannan sai muka ba mata masu yin abinci muka ba su Murahu da dubu 20 da za su kara jari da shi tun da daman suna yin sana’ar abincin. Bayan nan kaga a Jihar Jigawa an koya wa mata sana’o’in Dinki,Takalma da Jakunkuna, mun koya masu shirya Sarkoki na Dutse an kuma koya masu hada kayan sinadaran yin Girki ya yi kyau ya yi dadi, don haka ba abin da zamu ce da Gwamnanmu sai Sam barka.
Domin an debi mata Hamsin Hamsin daga kowace karamar hukuma aka ba su jari duk abin da nake gaya maka ba fa bashi bane. Na Awaki ne kawai bayan lokaci ya yi sai a karbi abin da aka ba mace na Awaki mata biyu da Namiji daya. Amma duk sauran da muke yi ba bashi bane muna yi ne kawai domin mata su samu ci gaba.
Sannan aka kawo ciyarwa na yan makaranta wanda Baba Buhari ya ce a ciyar da yan makaranta daga aji daya zuwa aji uku. To mu namu Gwamnan cikin adalcinsa sai ya ce ba za a ciyar da yara yan aji daya zuwa uku amma na hudu zuwa shida suna kallo ba saboda haka sai ya dauki nauyin ciyar da yara daga aji hudu zuwa aji shida mata aka baiwa domin su ne ke cin gajiyar abin a ciyar da yayanmu kuma su samu abin rikewa a hannu saboda haka mun gode masa Allah ya saka masa ya kuma saka masa da alkairi.
Garkuwa: To Mun gode kwarai
Kwamishiniya: Nima Na Gode.

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.