Home / Kasuwanci / ZA A KAFA KAMFANONIN TAKI, SHINKAFA A KATSINA

ZA A KAFA KAMFANONIN TAKI, SHINKAFA A KATSINA

Daga Taskar Labarai
Wasu matasa masu kishin jihar Katsina  sun yunkuro dan kafa wani katafaren kamfanin Taki a jihar Katsina. Kamfanin wanda yanzu haka an kammala ginin shi da yin nisa da saka kayan aiki ana aikin shi ne a Funtua,  inda yanki ne na noma sosai da kuma wasu kamfanonin manoma.
Kamfanin na karkashin kamfanin Greentide Agroservices Nig Ltd. Hadin gwaiwa ne na Alhaji Attahiru Bala Usman da Alhaji Ibrahim Bala Kuki.
Idan ya fara aiki ana sa ran zai rika samar da tan  449,280  000, duk shekara kusan Tan casa’in a kowace awa daya, zai kuma rika samar da takin NPK wanda za a rika amfani  da ma’adanan Uriya da sauransu.
Takin, wanda zai zama mai inganci daidai yanayin kasar noman da ake da ita, za kuma a samar da shi a farashi ingantacce tare da wadatar samuwar takin a duk lokacin bukatar shi. Daga jihar Katsina zuwa wasu jihohin musamman na arewa maso yamma.
Wannan kamfanin na taki, zai samar da aikin yi, sosai da ga na masu aiki kai tsaye da kamfanin zuwa yan sarin kayanshi da kuma ‘yan talla, wanda mafi yawan wadanda zasu amfana manoma ne, da matasa masu neman sana’a.
Wannan kamfanin ya dauko kwararru masana harkar daga kasashen waje wadanda zasu kula da aiki mai inganci ga fitar da takin.
Kafa kamfanin ya kai matakin karshe na samun amincewa daga gwamnatin tarayya.
Inda a satin da ya gabata 21/2/2020. Ma’aikatar kiyaye muhalli ta kasa, tayi zama don bin ka’idar kafa kamfanin kuma  zama ne na karshe, a Katsina.
A taron wanda jami’an ma’aikatar suka saurari bayanan daga jami’an kamfanin akan bin duk wata ka’ida da doka ta tanada.
Taskar Labarai ta ji cewa, kamfanin takin ya cika duk ka’idojin da suka dace, abin da ya rage masa saura tsare da kammala abin da ba arasa ba, da kaddamar da shi don fara aiki.
Wani kamfanin wanda hamshakin dan kasuwan nan na Katsina ya ke kokarin samarwa a Katsina shi ne na casar shinkafa mai suna Darma Rice Mills.
Kamfanin wanda yanzu ya kai matsayin kashi talatin cikin dari, na aikin gini a garin Dabaibayawa kusa da birnin Katsina. Shi yanzu yana matakin gina wajen ne.
Kamar yadda Taskar Labarai ta tabbatar, amma aikin ginin na tafiya sosai. Kamfanin mallakin Alhaji Dahiru Bara’u Mangal ne.
In aka kammala ginin aka sa kayan aiki, ana sa ran zai rika casar shinkafa  ton  dubu dari shidda a shekara. 600,000.
Zai samar da aikin yi na kai tsaye da saye da sayarwa, zai habaka noman shinkafa a Katsina. Zai dakile shigo da shinkafa ‘yar kasar waje.
Shima kamfanin ya samu amincewa ta ma’aikatar  tarayya ta kiyaye muhalli.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.