Home / Labarai / Gwamna Na Kogi Alhaji Yahaya Bello Allah Ya Saka Masa Da Alkairi – Shaikh Dahiru Bauchi

Gwamna Na Kogi Alhaji Yahaya Bello Allah Ya Saka Masa Da Alkairi – Shaikh Dahiru Bauchi

Mustapha Imrana Abdullahi
Fitaccen Malamin addinin Islama  da ke tarayyar Najeriya Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya yi addu’ar Allah ya saka wa Gwamnan Jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello da alkairi.
Shaikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi wa Gwamna Yahaya Bello da Gwamnan Jihar Bauchi Dokta Bala Muhammad kauran Bauchi addu’a ne a gaban dimbin mutanen da suka halarci babban taron Maulidin haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W) da aka kiyasta sun kai mutum miliyan biyar da aka yi a Bauchi
Shaikh Dahiru Bauchi ya kuma yi wa dimbin jama’a addu’a da suka taru a wannan wurin.
Shaihin ya kuma yi addu’ar ne inda ya maimaita har sau sama da biyar yana mai cewa Gwamnan Jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello Allah ya saka masa da alkairi.
Hakazalika ya kuma yi wa Gwamnan Jihar Bauchi Kauran Bauchi Alhaji Dokta Bala Muhammad Addu’ar shi ma Allah ya saka masa da alkairi.
Shima da ya tofa albarkacin bakinsa Gwamnan Jihar Bauchi da ya tashi ya maimaita irin abin da Shaikh Dahiru Bauchi ya fadi ne na yi wa Gwamnan Kogi addu’ar Allah ya saka masa da alkairi.

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.