Home / Labarai / Gwamna Radda Ya Koka Da Cewa  22 LGAs Marasa lafiya A Katsina

Gwamna Radda Ya Koka Da Cewa  22 LGAs Marasa lafiya A Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Radda ya koka kan matsalar tsaro a jihar Katsina, inda ya ce kananan hukumomi 22 daga cikin 34 da ke jihar ba su da lafiya sakamakon dimbin matsalar tsaron da ake fama da shi.

Gwamna Radda ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido ga Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, a hedikwatar ‘yan sanda, da ke  Abuja, a ranar Juma’a.

Ibrahim Kaula Mohammed, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Radda, a cikin wata sanarwa ya ce, Radda ya lura cewa kananan hukumomi Takwas daga cikin kananan hukumomin sun yi iyaka da dajin Rugu, wanda dalilin hakan yan Ta’adda ke amfani da hakan a matsayin wata dama a mafakar ‘yan bindiga, saboda hakan ne  Gwamnan ya nemi karin goyon baya daga ‘yan sanda don duba lamarin, kamar yadda ya dace da nufin a magance shi.

Wani bangare na sanarwar ya kara da cewa, “ya ​​yaba kokarin da rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ke yi, Gwamnan ya ce ya kai ziyarar ne domin karfafa zumuncin da ke tsakanin gwamnatin jihar Katsina da ‘yan sanda, da nufin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.

“Da yake nuna rashin amincewa da hare-haren wuce gona da iri da ‘yan bindiga ke kaiwatarwa al’umma, Gwamnan ya lura cewa kananan hukumomi 22 cikin 34 na Katsina na fama da matsalar rashin tsaron da ke yin barazana da tattalin arziki da rayuwar jama’a.

“Wannan, inji shi, ya samo asali ne daga wani daji mai tsawon sama da kilomita 800 da ke iyaka da kananan hukumomi takwas na jihar.

“Duk da haka, tuni gwamnatinmu ta dauki matasa 1,500 da a halin yanzu da ke samun horo kan yadda za su hada kai da jami’an tsaro wajen yaki da rashin tsaro a jihar.
“Shin zan iya amfani da wannan dandalin domin in gayyace ku zuwa bikin faretin domin kammala samun horo na  jami’an Community Watch Corps da ke shirin kammala horon su.

“Hakika, halartar taron rufewar zai kara kwarin gwiwar mambobin kungiyar.

“Da yake mayar da jawabi shugaban rundunar Yan Sandan Najeriya ya nuna godiya ga Gwamnan tare da bada tabbacin cewa ziyarar tasa za ta zama kwarin gwiwa ga rundunar ‘yan sandan Najeriya, a kokarinta na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

“Ya yaba da kokarin Malam Dikko Radda na magance matsalolin tsaro a Katsina.

“Shugaban ‘yan sandan ya ba da tabbacin cewa jihar Katsina za ta kasance cikin jihohi shida da za su ci gajiyar sa hannun na musamman ga hukumomin tsaro, da fadar shugaban kasa za ta yi.

About andiya

Check Also

Dangote cement export of clinker, cement increase by 87.2%

  Management of Dangote Cement Plc has revealed that the company dispatched seven ships of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.