Home / Big News / Gwamna Tambuwal Ya Karyata Batun Nadin Korede Mai Taimaka Masa

Gwamna Tambuwal Ya Karyata Batun Nadin Korede Mai Taimaka Masa

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya Karyata batun nadin Maryam Aliyu Obaje da ake wa lakabi da Korede inda ya bayyana lamarin bayanin nadin a matsayin karya kawai.
Tambuwal ya ci gaba da cewa shi babu wani batun nadin mai taimaka masa na musamman a kan kafofin sada zumunta na zamani domin shi bai yi nadin ba Sam Sam.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da mai bashi shawara a kan harkokin yada labarai da hulda da yan jarida Muhammad Bello ya Sanya wa hannu a garin Asaba na Jihar Delta.
Kamar yadda Gwamnan ya ce wanda a halin yanzu yake can Jihar Delta domin wata ziyarar aiki ta musamman ya tabbatar da cewa babu wani nadi mai kama da haka da shi ya yi don haka lamarin jita jita ce kawai ba gaskiya a ciki.
Sai ya yi kira ga daukacin jama’a da su yi watsi da abin da wadansu mutane ke yadawa a kafafen sada zumunta na zamani ko a duk wata kafar yada labarai.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.