Home / Labarai / Gwamna Tambuwal Ya Karbi Yan asalin Jihar Sakkwato Da Suka Dawo Daga Ibadan

Gwamna Tambuwal Ya Karbi Yan asalin Jihar Sakkwato Da Suka Dawo Daga Ibadan

Gwamna Tambuwal Ya Karbi Yan asalin Jihar Sakkwato Da Suka Dawo Daga Ibadan

 

 

Mustapha Imrana Abdullahi

 

Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga takwarorinsa da sauran shugabanni da suke a Nijeriya da kowa ya yi dukkan mai yuwuwa domin rungumar yan kasa baki daya.

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin gidan Gwamnati da ke Sakkwato lokacin da ya karbi yan asalin Jihar da suka Dawo daga garin Ibadan na Jihar Oyo sakamkon irin tashin hankalin da ya faru a kwanan nan.

 

Gwamnan ya bayyana lamarin da ya faru a Ibadan da cewa abin bacin rai ne da kuma abin da ke faruwa a wasu bangarori daban daban na kasar nan a yau, ya ce “A matsayin mu na yan kasa duk mun Sani cewa kowane mutum na da yancin zama a inda yake bukata cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk inda mutum ya zaba”.

 

“Wannan tanaji ne da ke cikin kundin  tsarin mulki, kuma duk mun Sani cewa idan akwai tashin hankali mutane za su rika tafiya zuwa garuruwan iyayensu na asali”, ya yi duba  da cewa ya dace ne kowane bangare na kasar nan yakamata ya zama gida ne ga kowa dan kasa kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin kasa”.

 

“Nijeriya kasar mu ce. Mun kuma San kalubalen mu. Wannan lokaci ne na kalubalen da ke gabanmu don haka ya zama wajibi mu hada kai da Juna domin ganin mun samu mafita ga matsalolin da suke cikin kasa”,. Inji shi.

 

Gwamnan ya kuma shawarci masu yin kausasan kalamai masu rura wutar da su hanzarta barin irin wadannan kalaman. “Ya dace a rika ganin mu muna samar da shugabanci tare da rungumar kowa baki daya a duk inda muka samu kanmu.Muna bukatar yin jan hankali a kan zaman lafiya kuma mu rika aikata shi”, Gwamnan ya kara da yin bayani

 

Gwamna Tambuwal ya bayar da misalin cewa Gwamnatin Jihar Sakkwato ba ta nuna bambanci ko kadan ga wadanda ba yan asalin Jihar ba duk ana daukar kowa dan Nijeriya ne musamman wajen biyan kudin makaranta, mallakar gida,wajen batun kula da lafiya a asibitoci da sauran abubuwa daban daban.

 

“Duk wanda ya zabi yazo Sakkwato ya zauna idan yana son ya Sanya dansa a makarantar Gwamnati ba mu yi masa wani cajin kudi daban. Kuma duk abin da dan asalin Jjhar Sakkwato yake amfani da shi na karatu kamar Samar da litattafai kyauta da sauran dukkan kayan koyon karatu, duk ana ba kowane mutum kyauta kamar dai yadda muke yi wa yan asalin Jihar Sakkwato, Gwamnan ya jaddada hakan.

 

Gwamnan ya bayar da tabbaci ga wadanda suka dawo din cewa Gwamnati za ta ba su harin da za su ci gaba da yin kasuwancinsu a cikin Jihar, Gwamnan ya kuma yi bayanin irin yadda ya dauki lamarin a lokacin da ya samu kiran waya a game da faruwar lamarin musamman a kan halin da mutanenmu suke ciki.

 

Ya ce ya bayar da umarni ga kwamishinan da ke kula da harkokin tsaro da ya hanzarta kiran wadansu mutane a Jihar Oyo domin shirya dawowa da wadanda lamarin ya rutsa da su.

 

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Kaddamar Da Manyan Ayyuka A Bakura Da Maradun

A ci gaba da gudanar da bukukuwan cika shekara ɗaya a karagar mulkin jihar Zamfara, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.