Home / Big News / Allah Ya Yi Wa Dokta Junaid Mohammed Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Dokta Junaid Mohammed Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Dokta Junaid Mohammed Rasuwa

 

Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Kano Arewacin tarayyar Nijeriya na cewa Allah ya yi wa Dokta Janaid Mohamamed rasuwa.
Wannan sanarwar dai ta fito ne daga dan uwan marigayin Dokta Ahmed Salik, wanda ya kasance tsohon dan majalisar wakilai ne da ya wakilci mutanen karamar hukumar Dala a cikin birnin Kano, daga shekarar 2003 zuwa 2007, kuma tsohon Malami a jami’ar Bayero da ke Kano.
Shi dai marigayi Dokta Junaid Mohammed ya taba zama dan majalisa a lokacin jamhuriya ta biyu karkashin jam’iyyar PRP, ya kuma rasu ne da Yammacin wannan rana ta Alhamis a gidansa da ke Kano bayan rashin lafiya”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Shi dai marigayin ya samu horon karatun zama Likita ne a tarayyar Sobiyat inda ya samu zama Likita, ya kuma zama daya daga cikin Dattawan arewacin Nijeriya da kasa baki daya da maganarsa ta zama wani abun dubawa ayi nazari sosai domin ingancinsa kasancewa jama’a tare da Gwamnati duk sun san muhimmancin maganar da ya kan yi.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.