Home / MUKALA / GWAMNA UBA SANI YA BUNKASA HARKAR WASANNI A JIHAR KADUNA

GWAMNA UBA SANI YA BUNKASA HARKAR WASANNI A JIHAR KADUNA

Imrana Abdullahi
A duk inda ake batun maganar harkokin wasanni ana batu ne da samun ingantacciyar lafiyar da za a yi amfani da ita, kasancewar sai da lafiya ake iya samun damar gudanar da harkokin wasanni daban da ban, don haka ne a hasashen dimbin masana harkar kiwon lafiya ke cewa bunkasa harkokin wasannin da Gwamnan Jihar Kaduna ya yi ya inganta harkar lafiya ne da kuma bunkasa tattalin arzikin jama’a baki daya.
Kamar dai irin yadda masana harkar wasanni a tarayya Najeriya ke cewa ba a taba samun wanda ya bunkasa harkokin wasanni daban daban a Jihar Kaduna kamar yadda Gwamna mai ci a halin yanzu Sanata uba Sani yake aiwatarwa ba.
Domin a kokarinsa ne ma ya samar da wadansu tsare tsaren da aka yi a fagen wasanni iri daban daban, kamar yadda a halin yanzu ya ware makudan kudin da za a yi aikin mayar da filin wasa na garin Kaduna wato ” Kaduna township stadium”, ya zama babbar cibiyar wasanni kala daban daban da suka hada da Damben Turawa, ( wrestling) wurin yin tarurtuka da dai sauran gudanar da wasanni kala kala.
Ga kuma yadda Gwamna Sanata Uba Sani ya karbo filin wasa na tunawa da marigayi Ahmadu Bello da ke cikin garin Kaduna wanda a da can ya na hannun Gwamnatin tarayya ne kuma tuni aka ware masa makudan kudi har naira biliyan biyu da za a yi wa filin gyara na musamman ta yadda zai tserewa tsara a rukunin filayen wasanni da ake da su a fadin Najeriya.
A cikin wannan makalar za a iya samun abubuwa daban daban da zamu kawo maku da aka samu nasarar ciyar da wasanni gaba a Jihar Kaduna.

Duk a cikin kokarin bunkasa harkokin wasannin ne yasa Gwamna Sanata Uba Sani ya nada Farfesa Benjamin Goghan da kuma Sa’idu Dibis, a matsayin kwamishinan wasanni da kuma mataimaki na musamman a harkar wasanni a Jihar Kaduna, ko a wannan kawai za a duba hakika za a tabbatar da cewa Gwamna Uba Sani ya jajirce sosai domin canza fuskar wasanni a Jihar Kaduna ta yadda al’amura za su bunkasa.

Saboda da zaran an ambaci sunan Sa’idu Dibis, ba a alakanta shi da komai sai harkar wasanni kawai, domin a 2009 ya kawo kulab din wasa na Super Eagle suka buga wasa a Kaduna kuma shi ne ya kawo kungiyar wasan DSS ta Sa’idu Pela duk sun yi wasa a Kaduna.
A nan kuma ya zama wajibi a yi wa Gwamna Uba Sani godiya bisa kokarin ciyar da harkar wasanni gaba, kamar yadda masu yin fashin bakin al’amura a kan harkokin wasanni ke cewa ne duk irin nade – baden da Gwamna Uba Sani, ya yi ba kamar na Sa’idu Dibis, domin  hakan ya nuna a fili cewa ana kishin ci gaban harkokin wasanni.
Wanda sakamakon hakan ne kafar yada labarai ta Hamada Radiyo da Talbijin karkashin jagorancin Ambasada Yusuf Mamman  suka bayar da lambar karramawa ta mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna a kan harkokin wasanni Sa’idu Dibis, a gaskiya kamar yadda masana harkokin wasanni ke cewa Gwamna Sanata Uba Sani ya yi matukar basira da ya kirkiri ofishin mataimaki na musamman a kan harkar wasanni kuma ya nada Sa’idu Dibis, domin a can baya an dauka ana samar da ofishi ne kawai domin a taimakawa wanda aka ba ya rika samun wani abin batarwa,  amma a halin yanzu sai muka ga ashe ba haka abin yake ba kasancewar Sa’idu Dibis jajirtacce ne a kan harkokin wasanni tare da bunkasa su baki daya a koda yaushe.
Duk wannan ci gaban da ake samu za a iya cewa basirar Uba Sani ce yadda aka samu harkar wasanni na kara bunkasa a Jihar Kaduna domin inganta tattalin arzikin kowa a Jihar.
Wannan makalar Imrana Abdullahi ne ya rubuto ta bayan gudanar da wani bincike.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.