Home / Labarai / Gwamna Uba Sani Ya Yi Sabbin Nade-nade

Gwamna Uba Sani Ya Yi Sabbin Nade-nade

Daga Imrana Abdullahi

A kokarinsa na cika alkawuran yakin neman zabensa ga al’ummar Jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani ya amince da sabbin nade-nade a ma’aikatu da hukumomi gwamnati daban-daban.

Yayin da yake taya sabbin wadanda aka nada, Gwamna Sani ya bukace su da su yi fice ta hanyar samar da tsare-tsare da tsare-tsare da za su amfani al’ummar jihar Kaduna.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da Muhammad Lawal Shehu, babban sakataren yada labarai na gwamna Uba Sani ya sanya wa hannu, kuma ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis 16 ga watan Agusta, 2023.

Ya kara da cewa dole ne su yi wa al’ummar Jihar Kaduna hidima da kwazo da da’a da kuma gaskiya.

Wadanda aka nada sun hada da

1. Umar Waziri – Mashawarci na Musamman a kan Al’amuran Kudi

2. Umar Baba Bambale – Mashawarci na Musamman, Magunguna

3. Farfesa Aminu Ladan Sharehu – Shugaban Hukumar Hidima ta Karamar Hukumar.

4. Arc Abubakar Rabiu Abubakar – Manajan Darakta, Kamfanin Raya Da Kaddarori na Jihar Kaduna (KSDPC)

5. Hadith Yahaya Hamza – Manajan Darakta, a kamfanin masana’antu da harkokin kudi  (KIFC).

6. Injiniya.  Inuwa Ibrahim – Manajan Darakta, a kamfanin Sufuri na Jihar Kaduna.

7. Dokta Iliyasu Neyu – Babban Sakatare na Hukumar Kula da batun ciwon Sida ta Jihar Kaduna (KADSACA).

8. Dokta Usman Abubakar – Darakta Janar na Hukumar tabbatar da ingancin ya Jihar Kaduna (KSSQAA).

9. Dokta Bello Jamo – Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jiha (SPHCB).

10. Joseph O. Ike – Babban Sakatare, Ofishin Kariya da Magance cin zarafi na Jihar Kaduna (KADBUSA).

11. Mohammed Rili –Janar Manaja a hukumar bunkasa harkokin Noma ta Jihar Kaduna (KADA).

12. Rakiya A. Umar – Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Nakasa ta Jihar Kaduna

13. Usman Hayatu Mazadu – Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA).

14. Muhammed Mu’azu Mukaddas – Janar Manaja, Hukumar Ci gaban Al’umma

15. Dr Jamilu Haruna – hukumar kula da ilimin firamare ta Jihar Kaduna (SUBEB).

16. Maryam Abubakar – Babbar Darakta (Corporate Services), Kaduna State Development and Property Company Ltd (KSDPC)

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.