Home / Labarai / Gwamna Uba Sani Zai  Gina Gidaje Dubu 10,000 Domin Saukakawa Jama’a

Gwamna Uba Sani Zai  Gina Gidaje Dubu 10,000 Domin Saukakawa Jama’a

 

 

Daga Imrana Abdullahi

 

 

Domin cike gibin gidaje da ake fama da shi na kalubalen gidaje , gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Uba Sani ta ce za ta samar da rukunin gidaje 10,000 a fadin kananan hukumomin jihar 23 nan da shekaru hudu masu zuwa.

 

Babban sakataren ma’aikatar gidaje da raya birane ta jihar Kaduna, Malam Rabi’u Yunusa ne ya bayyana haka a ranar Litinin a wajen taron majalisar kasa da gidaje da raya birane karo na 12 da aka gudanar a Kaduna.

 

Taron ya kasance takensa: ‘Karfafa tsare-tsare na rance na gida da na kasa da kasa a matsayin mafita don bunkasa ababen more rayuwa na gidaje masu arha a karkashin shirin fatan alheri.’

 

A cewar babban sakataren, gwamnatin Sanata Uba Sani a jihar ta fito da tsare-tsare na raya kasa don samar wa talakawa gidaje a karkashin shirinta na sabunta birane.

About andiya

Check Also

KASUPDA Organizes Stakeholders Engagement Programme

Community in the approved regularization layouts areas in Kaduna Metropolis have been advised to co- …

Leave a Reply

Your email address will not be published.