Related Articles
Gwamna Zullum Ya Bankado Ma’aikatan Bogi Dubu 22, 556
Alƙaluman sun nuna kimanin ma’aikatan bogi 14,662 aka gano a ƙananan hukumomin jihar yayin da aka gano wasu malaman karya har 7,794 a ɓangaren ilimi.
Da ya ke gabatar da rahoton, shugaban kwamitin tantance malaman firamare, Dr. Shettima Kullima, ya ce, tantancewar ta samarwa jihar rarar kuɗi sama da miliyan 183 da suke zurarewa a iya ɓangaren malaman firamare kaɗai dake ƙananan hukumar 27 dake faɗin jihar.
Bayan karɓar rahoton ne kuma gwamna Zulum, ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne don inganta harkar ilimi a jihar Borno, kasancewar gwamnatinsa ta baiwa harkar ilimin firamare fifiko.
An fara tantance ma’aikata a jihar ta Borno tun a shekarar 2013 inda aka samo dubbanin ma’aikatan bogi. Gwamna Zulum ne ya yanke shawarar faɗaɗa tantancewar har zuwa ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar Borno guda ashirin da bakwai.