Home / Lafiya / Gwamna Zulum Ya Bayar Da Umarnin A Dauki Likitoci 40

Gwamna Zulum Ya Bayar Da Umarnin A Dauki Likitoci 40

Gwamna Zulum Ya Bayar Da Umarnin A Dauki Likitoci 40
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zullum, na ganin ya samar da ingantaccen tsarin kula da lafiyar jama’a ya bayar da umarnin kara daukar Likitoci 40 da kuma amincewa da a fadada asibitin Kwararru.
Gwamnan da ya bayar da umarnin a ranar Talata ya bayyana cewa yin hakan zai taimaka ganin irin yadda jama’a ke karuwa a koda yaushe a cikin Jihar.
Wannan umarnin da Gwamna Zullum ya bayar yazo ne bayan watanni hudu da ya amince da a dauki ma’aikatan kiwon lafiya dari 594, kuma daga cikinsu 86 suk Likitoci ne, 365 kuma masu aikin Nus Nus ne da ake cewa kannen likitici, 45 Masu kula da bayar da magani da wane irin magani ya dace Gwamnatin ta sayo a asibitocin Jihar sai guda 100 masu aikin kula da Gwaje gwajen marasa lafiya ne da sauran ma’aikatan da suke taimakawa wajen kula da lafiyar jama’a.
Zulum ya bayyana wannan mataki ne na daukar Likitoci 40 a ranar Talata bayan kammala taro da da ya yi da shugabannin asibitocin Jiha guda Bakwai (7) da kuma wadansu cibiyoyi masu kama da hakan da suke a cikin garin Maiduguri da karamar hukumar Jere.
Taron dai an yi shi ne cikin sirri, duk da nufin kara inganta harkar lafiya da zai dai-dai da irin tsare tsare da manufofin Gwamnatin da Zullum ke wa jagoranci.
Bayan taron, Gwamna Zullum undertook ya dauki yanayi da yadda asibitin kwararrun inda kuma ya bayar da umarnin a kara gina wadansu bangarorin asibiti domin rage cinkoson da asibitin yake da shi tun farko.
Gwamnan ya kuma zagaya wani filin da aka samar a kula da asibitin kwararru na Gwamnatin Jiha da za a yi amfani da shi wajen fadada asibitin na kwararru.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.