Home / MUKALA / Ziyarar Da Na Kaiwa Wamakko Babu Wata Dangantaka Da Siyasa – Inji Bafarawa

Ziyarar Da Na Kaiwa Wamakko Babu Wata Dangantaka Da Siyasa – Inji Bafarawa

Ziyarar Da Na Kaiwa Wamakko Babu Wata Dangantaka Da Siyasa – Inji Bafarawa
Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Dalhatu Bafarawa ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, shugaba a Jam’iyyar APC a Sakkwato, a kwanan nan bashi da nasaba da siyasa, saboda haka shi yana nan a matsayin mai biyayya ga Jam’iyyarsa ta PDP.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Sakkwato bayan da wata jarida ta ruwaito cewa ya na shirye shiryen barin PDP zuwa jam’iyyar mai mulki a Nijeriya da ke da shugaban kasa wato APC.
“Ziyarar da na kaiwa tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ba shi da wata nasaba da siyasa ko wani abu game da Jam’iyyarsa ko wani batun canza jam’iyyar siyasa.
“Ina nan a matsayin mai biyayya ga jam’iyyar karkashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal kuma mai kokari a PDP, don haka ba abin da zan yi da APC ko wani abin da take yi”, inji Bafarawa.
Ya ci gaba da bayani game da ziyarar da ya kai wa shugaban APC a Jihar Sakkwato a gidansa, ya na mai cewa ya je ne domin yi masa gaisuwar mutuwar da aka yi masa da dan uwansa ya rasu kwanan nan.
” Masu wallafa labarai ko karai rayi game da ziyarar ta’aziyyar da na kai suna yi ne kawai domin yarfen siyasa da ke kokarin samun tunanin jama’a su raja’a kansu domin kawai sun bayar da labari.
“Wannan ba shi ne karon farko da na kai wa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ziyarar gaisuwar ta’aziyya ba musamman a wannan lokaci na jaraba  wa da muke ciki”.
“Na je garin Wamakko domin yin ta’aziyyar rasuwar dan uwansa, marigayi Baraden Wamakko, kuma ko a lokacin da yarsa ta rasu, duk da yake na yi tafiya, duk da haka na tura wakilai na masu taimaka Mani domin su je su jajanta wa Wamakko a gidansa da ke Gawon Nama”.
“Bambance bambancen mu na siyasa, duk yadda suka kasance, ba su shafi dangantaka da ta dade a tsakaninmu ba da tausayawa Juna duk lokacin da wani abu ya samu dayanmu musamman a lokacin da waninmu ke fuskantar irin wannan kalubale.
“Shi da kansa ya kawo mini ziyara a Bafarawa domin yi mini ta’aziyya lokacin da na rasa mahaifina, marigayi Sarkin Gabas na Bafarawa, kuma haka yake kira na a waya a duk lokacin da irin wannan ta faru ga iyalai na ko ga wani dangina”, Bafarwa ya yi bayani domin a fahimta.
Tsohon Gwamnan ya bayyana bacin ransa a game da labarin wanda wadansu jaridun Nijeriya da ke fita kullum suka wallafa domin kawai a mayar da lamarin ziyarar da ya kaiwa Sanata Wamakko al’amarin siyasa.
“Wasu yan jarida suna yin aikin gaggawa su yi rubutu kuma su wallafa karya domin kawai ace sun bayar da labarai, Lamar yadda wani mai aiki da jaridar Daily trust a Sakkwato ya aikata domin kawai yin yarfen siyasa da batanci a gare ni”.
“ Ina nan ina yin biyayya ga jam’iyyata, ina biyayya ga Gwamna na Alhaji Aminu Waziri Tambuwal kuma ya ce zai yi dukkan mai yuwuwa domin samun nasarar Gwamna Tambuwal a lokacin Mulkinsa baki daya kuma duk wanda jam’iyyata ta tsayar a nan gaba”, kamar yadda ya tabbatar.

About andiya

Check Also

Dangote Refinery Aims for 500,000 Barrels Daily by July, eyes stock market debut

Also the chairman Aliko Dangote has equally announced intentions to list the refinery on the Nigerian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.