Home / Labarai / Gwamna Zulum Ya Karbi Yan Gudunhijira Dubu Biyar Daga Kamaru

Gwamna Zulum Ya Karbi Yan Gudunhijira Dubu Biyar Daga Kamaru

Gwamna Zulum Ya Karbi Yan Gudunhijira Dubu Biyar Daga Kamaru
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin da Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum take na ganin an dawo da yan Nijeriya gida daga kasar Kamaru a halin yanzu Gwamnan ya karbi yan Gudunhijira mutane dubu biyar (5000).
An kuma ba wadanda suka dawo din gidaje, abinci da kudi domin samun saukin rayuwa cikin inganci da walwala.
Jami’an Gwamnatin kasar Kamaru, karkashin jagorancin Ministan da ke kula da harkokin iyakokin kasa, Paul Atanga Nji,sun dawo da yan Nijeriya tare da mika kashin farko na mutane dubu biyar ga Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum.
Taron mika wadanda aka dawo da su din an yi shi ne ranar Litinin, a wani Takaitaccen taron da aka yi a Amchiide, wani gari da yake a kan iyaka tsakanin Nijeriya da Kamaru, kusa da garin Banki a karamar hukumar Bama a yankin Borno ta tsakiya.
Wadanda aka dawo da su din na cikin dubban mutane yan Nijeriya da suka yi Gudunhijira da suka kasance mafi yawa daga Jihar Borno, wadanda tun a shekarar 2014 suka tsere da kadan da kadan zuwa sansanin  Minawao a cikin Mokolo, wani yanki mai nisa da ke arewacin Kamaru, domin tsarewa matsalar yan Boko haram da ke kashe jama’a ba ji ba gani, amma wasu mutane na cewa a kalla mutane sama da dubu 60,000 sun tsere zuwa wannan sansani daga Jihar Borno da Jihar Adamawa amma dai a tsawon wasu shekaru yawan wadanda suka gudun ya ragu sakamakon damar da wasu suka samu suka koma garuruwansu.
Taron dai ya samu halartar wadansu manyan jami’ai daga kasar Kamaru da suka hada da Gwamnan yanki mai nisa na arewacin Kamaru Midjiyawa Bakary da jami’an hukumar kula da yan Gudunhijira na majalisar dinkin duniya, UNHCR.
Ministan kula da batun kan iyakokin Paul Atanga Nji Paul ya bayyana cewa shugaba Paul Biya ya amince da a ba wadanda aka dawo da su abubuwan da za su samu saukin rayuwa da suka hada da kayan abinci,Katifu, abin rufa da sauran kayan abinci ga dukkan mutane dubu 5,000 da aka dawo da su a matsayin tallafi.
Ministan ya kuma godewa Gwamna Zulum da ya ginawa yan gudunhijirar gidaje domin a nan ne za su zauna.
Gwamnan Zulum ya amince da bayar da kudi ya kuma zagaya domin ganin aikin ginin gidaje masu saukin kudi guda dubu 6,000 da ake yi a garuruwan Banki,Gwoza,Konduga, Kaga da sauran wadansu daban,da wasu kuma da aka kammala.Wadanda mafi yawansu an yi amfani da su ne domin tsugunnar da yan Gudunhijira da dai sauran wadanda aka tsugunnar.
Gwamna Zulum, a madadin Nijeriya sun yi wa shugaban kasar Kamaru godiya da sauran jami’an Gwamnatin kassr Kamaru da al’ummar da mutanen suka zauna a tare da su a tsawon shekaru shida. Gwamnan ya kuma bayyana farin cikinsa da taimakon da shugaba Biya ya bayar.
” Ina son mika cikakkiyar gamsuwa da farin ciki ga Gwamnatin Jihar Kamaru a karkashin jagorancin shugaban kasar Kamaru Paul Biya, bisa irin taimakon da aka ba yan Nijeriya da suka je Gudunhijira kasar Kamaru a Minawao, hakika muna godiya har cikin zukatanmu”, inji Zulum.
Wannan kokarin dawo da yan Nijeriya gida ana kokarin cimma yarjejeniyar taron da aka yi ne a ranar 10 ga watan Fabrairu 2021, a Marwa da ke kasar Kamaru da ya samu halartar mutane daga Kamaru,hukumar UNHCR da kuma wata tawaga saga Nijeriya da suka hada da Gwamna Zulum da jami’an ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje,da jami’an hukumar kula da yan Gudunhijira da samuwar wata matsala da kula da ci gaban rayuwar jama’a ta kasa, hukumar kula da sansanonin yan Gudunhijira da kula mai ba Gwamna shawara na musamman ga Gwamna Zulum a kan harkokin dubawa da kuma kididdige ayyuka, da ya jagoranci wani kwamitin da ya yi aikin dawo da yan gudunhijirar, Injiyaya Lawal Abba Wakilbe.
….Gwamna Zulum ya kuma rabawa wadanda suka dawo din abinci da kudi.
Bayan da ya karbi yan gudunhijirar, Gwamna Zulum a garin Banki inda ya kaddamar da rabon kayan abinci da kayan da ba na abinci ba ga yan Nijeriya dubu biyar (5,000).
An ba kowane Namiji da ke shugabanta wasu iyalai kudi naira dubu 30,000 an kuma ba kowace mace naira dubu 10,000 da kuma Atamfa.
Gwamnan ya nuna jin tausayinsa da irin yadda suka rayu a matsayin yan Gudunhijira, ya kuma ba su tabbacin cewa Gwamnati na tabbatar masu da tsaron lafiyarsu da jin dadin da kuma samar masu da kyakkyawar rayuwa su dawo kamar yadda suke kamar can baya.
Kwamishinan sake ginawa da aikin gyara da sake tsugunnar wa Injiniya Mustapha Gubio, kwamishinan ma’aikatar kula da kananan hukumomi da masarautun gargajiya Sugun Mai Mele, da tsohon kwamishinan gidaje da wutar lantarki Babagana Tijjani Banki duk suna cikin mutanen da ke cikin tawagar Gwamna Zulum.

About andiya

Check Also

Gwamna Radda Ya Koka Da Cewa  22 LGAs Marasa lafiya A Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Radda ya koka kan matsalar tsaro a jihar Katsina, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.