Home / Labarai / Gwamna Zulum Ya Rabawa Iyalai Dubu 40,000 Kayan Abinci Da Naira Miliyan 125.5 A Damboa

Gwamna Zulum Ya Rabawa Iyalai Dubu 40,000 Kayan Abinci Da Naira Miliyan 125.5 A Damboa

 Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Talatar da ta gabata ne ya rabawa iyalai da suka kai dubu 40,000 a garin Damboa Damboa abinci da makudan kudi naira miliyan 125.5 a hedikwatar karamar hukumar Damboa da ke yankin Kudancin Jihar Borno.
Ziyarar Gwamnan ta zo ne bayan kwanaki biyu da yan Ta’adda suka yi kokarin kai wa garin hari, inda aka samu nasarar tarwatsa da yawa daga cikinsu yayin harin da bai yi nasara ba.
Jerin mazajen da aka ba tallafin Buhunan abinci
Gwamna Zulum ya kwana a garin na Damboa ya na ta shirye shiryen yadda za a raba kayan jin kan domin taimakawa jama’a su samu saukin rayuwa.
Wadanda suka amfana da tallafin sun hada da magidanta dubu 14,900 da kuma Mata dubu 25,100 mafi yawansu duk sun rasa hanyar neman abincinsu kuma na za su iya zuwa Gona ba duk sun amfana daga wannan shirin.
Kowane daga cikin wadannan magidantan dubu 14,900  ya amfana da buhun Shinkafa, buhun Wake, su kuma Matan dubu 25,100 sun samu kudi dubu biyar (5,000) da turmin Zani kowaccensu.
Da yake magana da wadanda suka amfana, Gwamna Zulum ya bayyana masu cewa Shinkafar da aka ba su wani bangare ne na tsarin Gwamnatin tarayya na ba su tallafi daga hukumar kula da shigi da ficen kayayyaki ta kasa wato Kwastan.
Wadanda suka amfana su na dauke Buhunan abinci na Shinkafa da waje
Sai Gwamnan ya yi godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari game da irin tallafin da yake bayarwa ga Jihar Borno.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.