Home / Labarai / Gwamna Zulum Ya Yi Maraba Da Shugabannin Tsaro, Ya Godewa Buratai, Sadique Da sauransu

Gwamna Zulum Ya Yi Maraba Da Shugabannin Tsaro, Ya Godewa Buratai, Sadique Da sauransu

Gwamna Zulum Ya Yi Maraba Da Shugabannin Tsaro, Ya Godewa Buratai, Sadique Da sauransu
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jinjinawa shugaban kasa bisa nadin shugabannin hukumomin tsaron tarayyar Nijeriya.
 Gwamna Zulum ya kuma godewa shugabannin hukumomin tsaron da suka ajiye aiki musamman shugaban sojojin kasa da na sojojin Sama  Litanar Janar Tukur Buratai da Abubakar Sadique wadanda tare da su ne Jihar Borno ta yi aiki kafada da kafada wajen yaki da yan Boko Haram.
Zulum ya yi wannan magana ne a takaice a yammacin Talata a garin Maiduguri lokacin da wadansu yan jarida suka nemi jin ta bakinsa jim kadan bayan sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar cewa ta karbi batun ajiye aikin da shugabannin rundunonin tsaron Nijeriya suka yi.
Kuma har an nada wasu da za su ja ragamar rundunonin da aka nada Mejo Janar Leo Irabor shugaban rundunar yakin sojan kasa sai Mejo Janar Ibrahim Attahiru shugaban sojoji sai Ria Adimiral Awwal Zubairu Gambo shugaban sojojin Sama sai kuma Isiaka Oladayo Amao shugaban sojojin sama.
“Shugabannin rundunonin tsaron da suka ajiye aiki hakika sun kasance tare da mu har tsawon shekaru shida, a wannan lokaci an rika yin aiki da kuma samun kalubale mai yawa sun kuma taimaka wajen samun zaman lafiyar da muke jin dadinsa a yanzu ta hanyar fada da Boko haram, sun taimaka sosai wajen samun ci gaban da aka samu. Kokarin sake ginawa da kuma sake tsugunnar da ya samu nasara ne sakamakon aiki tare da Lutanar Janar Buratai da kuma Sadique, hakika da kuma aiki tukuru na sauran rundunonin tsaro, masu bayar da bayanan sirri, Yan Sanda da sauran jami’an tsaro baki daya da kuma yan sakai, ba zamu mance da wannan kokarin gudunmawar ba,don haka kamar yadda duk muka Sani komai na da lokacinsa, muna godiya ga dukkan shugabannin rundunonin tsaron da suka ajiye aiki domin gudunmawar da suka bayar muna yi masu fatan ci gaba da samun nasara a duk inda za su samu kansu a cikin harkokin rayuwa nan gaba”.
 “A game da wadanda suka maye gurbinsu kuwa musamman Janar Leo Irabor da kuma Janar Attahiru dukkansu sun yi aiki a nan Jihar Borno a matsayin shugabannin rundunar tsaro ta Lafiya Dole, don haka sun san dukkan abin da yake nan saboda haka muna tabbatar da cewa za su kara kwazon aiki domin a ci gaba da tabbatar da nasara, gwamnatin Jihar Borno za ta ba su dukkan goyon baya da hadin kan da suke bukata kamar yadda muka ba wadanda suka gaba ce su, za kuma mu ci gaba da yin abin da muke yi domin taimakawa Sojoji na samar da kaya kamar dai yadda muke yi, zamu ci gaba da wayar wa da jama’a kai domin samun bayanan sirri da kuma daukar nauyin dukkan masu aikin sakai, yin addu’a ga jami’an tsaron da suke karkashin biyan albashin Gwamnati da kuma na masu aikin sakai da kuma taimakawa iyalansu kamar dai yadda muke yi”, inji Zulum.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.