Home / KUNGIYOYI / Gazawar Masu Haya Da Babura Mai Kafa Uku Muke Kula Da Rasidi – Shehu Bello

Gazawar Masu Haya Da Babura Mai Kafa Uku Muke Kula Da Rasidi – Shehu Bello

Gazawar Masu Haya Da Babura Mai Kafa Uku Muke Kula Da Rasidi – Shehu Bello

Mustapha Imrana Andullahi
Shehu Bello, jami’i ne da ke kula da yadda ake tara kudin shiga a bangaren sayar da rasidin ababen hawa masu haya da Babur mai kafa uku da motocin Bus da ke zirga zirga cikin gari a yankin unguwannin Mando da yankin hayin Rigasa ya shaidawa manema labarai a Kaduna cewa gazawar masu haya da Babura mai kafa uku yasa Gwamnati ta ba su aikin kulawa da sayar da tikiti domin a samu nasarar aikin tun a matakin karamar hukuma.
Shehu Bello ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilinmu a Kaduna inda ya ce hakika akwai wani lokacin da aka kira taro domin tattaunawa da shugabannin yan kungiyar masu haya da motoci da masu haya da Babura.
” A wajen taron an tambayi masu haya da motoci ko za su iya Sayar da rasidi na ababen hawa da za su rika tara harajin Gwamnatin a kullum suka ce za su iya, amma da aka tambayi masu haya da Babura mai kafa uku sai suka ce su gaskiya ba za su iya ba wannan tasa aka dauki aikin aka ba su daga matakin karamar hukuma da wannan muke ce masu Allah ya saka masu da alkairi bosa irin kokarin da suke yi a kullum”, inji shi.
Ya kuma shaidawa wakilinmu cewa suna yin aiki tare da tsare ka’ida da girmama kowa ba wata matsalar hayaniya balantana a samu rashin jituwa da wani ko wasu, kuma suna gudanar da aiki ne daga safe zuwa karfe sha biyu, sha biyu da rabi sun tashi sai kuma Gobe.
Ya kara da cewa duk wani mai haya da Babur mai kafa uku da aka gani yana sayar da rasidi  Gwamnati lallai karya yake yi ba na domin irin wadannan masu haya da Babura masu kafa uku ba su da wani hakki a sayar da rasidi  Gwamnati don haka kowa ya kiyaye, domin idan ba a kiyaye ba hakika lamarin zai zama da matsala domin tun daga matakin karamar hukuma za a dauki matakin da ya dace.
Bayanin hakan ya biyo bayan irin yadda aka samu takaddama tsakanin wani Direban Babur Mai kafa uku da wani mai shugabancin tashar Babura mai kafa uku bangaren ACOMARAN.
Zamu kawo maku karin bayani nan gaba.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.