Home / Labarai / Gwamna Zulum Zai Mayar Da Kananan Hukumomi 5 Manyan Birane A Jihar Borno

Gwamna Zulum Zai Mayar Da Kananan Hukumomi 5 Manyan Birane A Jihar Borno

Gwamna Zulum Zai Mayar Da Kananan Hukumomi 5 Manyan Birane A Jihar Borno
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin ganin al’ummar da ke zaune a kananan hukumomi biyar cikin Jihar Borno sun zama manyan biranen da za a iya yin alfahari da su ko’ina a fadin duniya Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum ya lashi takobin ganin an samu nasarar wanann aikin.
Gwamna Zulum ya rabawa mutane kayan abinci da kudi ga yan gudunhijirar da ke zaune a Mafa har mutum Dubu 9,400 da nufin su samu saukin rayuwa.
 Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana hakan ne a kokarin tabbatarwa da jama’a tsarin Gwamnatinsa na mayar da wadansu kananan hukumomi biyar su zama biranen da za a yi tunkaho da su a duk fadin duniya.
Al’ummar da ke a Biu, Gubio, Kaga, Mafa da Monguno su ne aka ware domin fara aikin mayar da wuraren birane kashi na farko, ya kuma bayyana hakan ne a ranar Asabar lokacin da ake ci gaba da aikin rabon kayan jinka ga dimbin jama’a a Mafa.
 “Mun fara aikin mayar da wasu garuruwa su zama birane kuma mun fara da kauyuka da garuruwa a kananan hukumomi biyar. A kowace kuma za mu gina gidaje da ma’aikata za su samu wurin zama cikin gidaje ginin zamani. Kananan hukumomin kuma sun hada da Gubio, Biu, Kaga,Monguno da Mafa a cikin tsarin kashi na farko”, Inji Zulum.
Gwamnan dai ya Isa garin Mafa ne a ranar Juma’a, saga Damasak inda ya kwana a daren Alhamis
  A Mafa, inda ya kara kwana, Gwamna Zulum a daren ranar Juma’a, ya kai ziyarar bazata babban asibitin inda ya kuma tarar da wadansu zaratan ma’aikatan kula da kiwon lafiyar jama’a daga cikinsu har da wata mace yar kabilar Ibo mai suna Misis Mabel Ijeoma daga Jihar Anambara da take aiki a wurin tsawon shekaru sha biyar (15) ta kuma samu kyautar kudi kamar kowa naira dubu dari biyu daga wurin Gwamnan.
A ranar Asabar Gwamnan ya Sanya idanu ga aikin rabon kayan abinci da kudi ga mutane dubu Tara da dari hudu ga wadanda suke Gudunhijira.
Kowane daga cikin mutane dubu uku da dari biyar daga jerin  Maza ya samu buhun Shinkafa da buhun Masara da kuma kudi, sannan kuma kowace Mace daga cikin mata dubu biyar da dari Tara sun samu turmin Zani, fakitin Suga biyu da kudi.
Gwamna Zulum daga nan ya kuma duba aikin gine ginen da ake yi da ya hada da aikin Noman rani da kuma aikin horar da mutane koyon sana’o’i da kuma aikin gina shaguna da tashar mota da ke dauke da shaguna 150.
Zulum ya kuma shawarci al’ummar da su dauki wannan a matsayin wata damar yin addu’o’i da nufin samun dawowar zaman lafiya a Jihar Borno da kasa baki daya.
“Ya kuma yi ga daukacin al’ummar da su kara himma wajen yin addu’o’I a wannan watan na Ramadana domin samun dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar, Nijeriya”, Zulum ya shawarci jama’a.
Gwamnan ya kuma yi godiya ga hukumar Gwamnatin tarayya da ke aiki domin ci gaban yankin arewaci ta Gabas bisa taimakawa aikin Gwamnatin Jihar.

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.