Home / Uncategorized / Gwamnaatin Yobe Ta Yi Alƙawarin Kammala Ayyukan Da Ta Fara Tare Da Kaddamar Da Wasu Ayyukan

Gwamnaatin Yobe Ta Yi Alƙawarin Kammala Ayyukan Da Ta Fara Tare Da Kaddamar Da Wasu Ayyukan

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
A zaman majalisar zartaswar Jihar na farko da ta gudanar a wannan shekara ta 2025  majalisar zartaswar Jihar Yobe karkashin jagorancin gwamna Mai Mala Buni ta yi alƙawarin kammala dukannin ayyukan da ta fara tare kuma da kaddamar wasu muhimman ayyukan raya kasa a sassan Jihar.
Bayanin hakan ya fito ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar ta laraba Jim kadan da kammala wannan zama na majalisar zartaswar wadda kwamishinan harkokin cikin gida, yada labarai da al’adu na jihar Alhaji Abdullahi Bego ya gabatar.
A cewar sa, gwamnatin jihar Yobe ta bayyana shirye-shiryenta na kammala tare da kaddamar da wasu ayyuka da tun farko ta ke da tsaka da yin su a wannan shekara ta 2025.
Majalisar zartaswar  jihar ta bayyana irin nasarorin da gwamnatin ta samu a shekarar 2024 tare da bayyana manufofinta na shekara mai zuwa.
Cikin muhimman ayyukan da gwamnatin ta gudanar sun kunshi na harkokin kasuwanci yadda ta ke gina manya-manyan kasuwannin zamani don habaka kasuwanci a garuruwan  Potiskum, Ngalda, da Yunusari kasuwannin sun kusa ƙarewa, inda kasuwar zamani ta garin na  Potiskum da sauran kasuwannin biyu aikin su suka kammalu da kimanin  kashi 90%, sai kasuwar zamani ta Geidam da aikin ta ya kai  kashi 75%.
Haka nan gwamnatin ta kuma gina kamfanonin sarrafa ridi a garuruwan Machina,  Damaturu, Nguru da Potiskum.
Kan abin da ya shafi gina hanyar mota kuwa, ana ci gaba da gudanar da manyan ayyuka da dama da suka hada da titin Fika-Maluri, titin Kukuri-Chukuriwa-Dawasa, da babban titin Karasuwa-Galu- zuwa Gashu’a da dai sauransu bayan titunan motar da tun tunin aka kammala su.
Kan abin da ya shafi titunan cikin garuruwa kuwa, a cewarsa gwamnatin ta kammala aikin titunan garuruwan Nguru, Jajimaji, Gashu’a, Potiskum, Damagum, Damaturu, Buni-Yadi, Babban Gida, da Geidam, tare da gudanar da ayyuka a garuruwan Fika, Buni-Yadi, da Yunusari.  .
Gwamnatin jihar ta kuma  samu tallafin kayayyakin kiwon lafiya da kungiyar agajin lafiya ta duniya (World Medical Relief a Amurka ta bayar, wadanda suka hada da gadajen asibiti, famfunan ruwa.
Gwamnaatin ta kuma tallafa wa daliban da ke karatu a kasar Indiya,  duk da kalubalen  yanayin da ake fuskanta.
Zamantakewar Damaturu babban birnin jihar gwamnatin na da kudirin gudanar da wani babban shiri a shekarar 2025 wajen gudanar da muhimman ayyukan raya kasa.
Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana jin dadinsa ga ‘yan majalisar kan rawar da suka taka wajen ganin an samu nasarar aiwatar da kasafin kudin shekarar 2024, wanda ya sa jihar Yobe ta kasance daya daga cikin jihohin da suka fi iya aiki a kasar nan.
Don haka gwamnan ya bukaci majalisar ta ci gaba da jajircewa wajen isar da karin ayyuka ga al’ummar jihar Yobe a wannan sabuwar shekara ta 2025.

About andiya

Check Also

Senator (Barr) Sunday Marshall Katung decries Abduction Of 22 Women And Children

As a result result of too much security challenges in some local Governments in Kaduna …

Leave a Reply

Your email address will not be published.