Home / Labarai / Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya Ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya

Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya Ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya

 

Daga Imrana Abdullahi

 

Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya zama shugaban kungiyar Gwamnonin arewacin Najeriya.

Majiyarmu ta tabbatar mana cewa Gwamnan Gombe dai ya samu nasarar lashe zaben Gwamnan Jihar da ke jiran rantsuwa domin ci gaba da zama Gwamnan Jihar Gombe a karo na biyu, a ranar 29, ga watan Mayu.

Hakan kuma ya biyo bayan kammala wa’adin Gwamnan shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa ne na yanzu Simon Bako Lalong da wa’adin Mullins a matsayin Gwamna ke karewa a ranar 29 ga watan Mayu.

Ana saran Gwamna Muhamamd Inuwa Yahaya ana saran zai shugabanci kungiyar domin ciyar ga yankin arewacin Najeriya gaba.

Kuma wannan shugabanci da ya same shi ya biyo bayan irin yadda Gwamnan na Gombe Gombe samu gagarumar nasara ne a karon farko a fannonin Ilimi,lafiya da kuma tattalin arziki duk sun bunkasa a Jiharsa.

Kuma kamar yadda kowa ya shaida Jihar Gombe ce wurin da aka fi samun zaman lafiya a yankin Arewa maso gabashin Najeriya a tsawon shekarun nan hudu da ya jagoranci Jihar.

Zamu kawo maku karin bayani…

About andiya

Check Also

Northern govs meet in Kaduna, design regional economy, human capacity devt

    The chairman, Northern States Governors’ Forum (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, has called for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.