Home / Ilimi / Gwamnan Jihar Akwa Ibom Ya Bayar Da Umarnin Yin Binciken Abin Da Ya Faru A Makarantar Deeper Life

Gwamnan Jihar Akwa Ibom Ya Bayar Da Umarnin Yin Binciken Abin Da Ya Faru A Makarantar Deeper Life

Gwamnan Jihar Akwa Ibom Ya Bayar Da Umarnin Yin Binciken Abin Da Ya Faru A Makarantar Deeper Life
Mustapha Imrana Abdullahi
Sakamakon irin korafe korafen da wadansu iyayen yara suka yi game da abin da ya samu dansu dalibi a makarantar kwalejin Deeper Life da ke Uyo.
Gwamnan Jihar ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan abin da ya faru ga wannan dalibin makarantar, wannan korafi dai Gwamnatin ta same shi ne ta hanyar kafafen yada labaran sadarwar zamani da kuma wadanda aka saba da su tun asali suna fadakar da jama’a.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai da tsare tsare kwamared Ini Ememobong da aka rabawa manema labarai.
Inda iyayen suna bayyana irin yadda aka tozarta yaron na su kasancewarsa dalibi a makarantar da abin ya faru a makarantar.
Bisa faruwar hakan ne Gwamnan Akwa Ibom Mista Udom Emmanuel ya bayar da umarni ga kwamishinan ilimi a gudanar da bincike kan lamarin, kuma a dauki matakin da ya dace ba tare da bata lokaci ba.
Gwamnatin Jihar dai a shirye take a koda wane lokaci su kare hakkin kowane yaro kamar yadda tsarin mulki ya tanadar mata.

About andiya

Check Also

SARDAUNAN FUNTUWA ALHAJI AKILU HASSAN YA YI KIRA GA AL’UMMA SU TASHI TSAYE WAJEN YIN ADDU’O’I

Daga Abdullahi Sheme  Alhaji Akilu Babaye Daraktan kamfanin rukunin NAK kuma Sardaunan sarkin Maskan katsina …

Leave a Reply

Your email address will not be published.