Home / Lafiya /   Masu Matakin Albashi Kasa Da 14 Su Yi Aiki Daga Gida – El- Rufa’I

  Masu Matakin Albashi Kasa Da 14 Su Yi Aiki Daga Gida – El- Rufa’I

Masu Matakin Albashi Kasa Da 14 Su Yi Aiki Daga Gida – El- Rufa’I

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I ta bayar da sanarwar cewa dukkan wani da yake kasa da matakin Albashi na 14 su ci gaba da yin aiki daga gidajensu daga ranar Litinin 21 ha watan Disamba, 2020.
Kamar yadda Gwamnatin ta bayar da sanarwa cewa wannan matakin zai iya kasancewa yana da dangantaka da idan wani shugabansu a wurin aiki ya bukaci su zo wurin aiki wato a ofishinsu.
Kamar dai yadda Gwamnatin tuni ta bayar da sanarwar cewa ya zama wajibi ga dukkan jama’a su kasance idan suna cikin gida tare da mutane masu yawa ko sun fita daga cikin gidajensu su Sanya Takunkumin rufe hanci da baki.
Su kuma rika bayar da tazara a wuraren hidimar jama’a ko a motocin haya ko abin hawa Babura masu Kafa uku.
A rika wanke hannu a kai a kai da sabulu ko abin wanke hannu da kamfanonin da aka amince da su suka samar domin amfanin jama’a saboda akwai sinadarin kashe kwayoyin cuta.
Gwamnatin dai na bukatar jama’a su ci gaba da kiyaye dukkan ka’idojin da aka shimfida domin yaki da wannan cuta da ta addabi duniya baki daya.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.