Home / Labarai / Gwamnan Jihar Zamfara Ya Bada Umarnin A Biya Albashi Da Kudin Alawus Alawus

Gwamnan Jihar Zamfara Ya Bada Umarnin A Biya Albashi Da Kudin Alawus Alawus

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya bayar da umarnin a biya daukacin ma’aikatan Jihar kudin albashinsu da kuma kudin alawus alawus domin al’ummar Jihar su samu sukunin yin bukukuwan Sallah cikin walwala da annashuwa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwar da ke dauke da sa hannun babban Sakataren ma’aikatar kudi S. Mohammad da aka rabawa manema labarai.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa umarnin ya fara aiki ne a ranar Juma’a nan.

About andiya

Check Also

An Zargi PDP Da Ayyukan Ta’addanci A Jihar Zamfara

Gamayyar Kungiyoyin Kwararru Na Dattawan Arewa Sun Kalubalanci Kalaman PDP A Game Da Batun Tsaron …

Leave a Reply

Your email address will not be published.