Home / Labarai / Gwamnan Kaduna Da Shugaban Majaliaa Abbas Tajudeen Sun Yi Alakawarin Yin Aiki Tare Domin Ci Gaban Jiha Da Kasa Baki Daya

Gwamnan Kaduna Da Shugaban Majaliaa Abbas Tajudeen Sun Yi Alakawarin Yin Aiki Tare Domin Ci Gaban Jiha Da Kasa Baki Daya

 

 

Daga Imrana Abdullahi

Shugaban majalisar wakilai Dokta Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa ya na jin dadin irin goyon bayan da yake samu daga Jiharsa wanda shugabannin siyasa ke bashi, da suka hada da Gwamna Uba Sani mai ci a yanzu da kuma tsohon Gwamna Malam Nasiru Ahmes El- Rufa’I ta yadda Jihar za ta ci gaba da kasa baki daya.

 

Shugaban majalisa Abbas ya ci gaba da bayanin cewa irin goyon bayan da yake samu daga Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani, El- rufa’i da ministan muhalli Malam Balarabe Abbas Lawal hakika na kara masa kwarin Gwiwa wanda hakan ne ya bashi karfin Gwiwar neman shugaban majalisar wakilai ta kasa, tun kafin zaben shekarar 2023 da ya gabata.

 

 

Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin gwamna Una Sani a ofishinsa a ranar Laraba.

 

Gwamnan ya jagoranci wata tawaga ce mai karfi ta al’ummar Jihar da suka kaiwa shugaban majalisar wakilai ziyara.

 

 

Ya kuma samu rakiyar Malam Balarabe Lawal, sai kuma wani babban mashawarci a cikin majalisar zartaswar Jihar Kaduna Alhaji Hamisu Abubakar Abubakar sauran manyan mataimakan Gwamnan

 

Shugaban majalisar Abbas, cewa ya yi ” hakika wannan abin karfafa Gwiwa ne da farin ciki kasancewar a wannan watan na Janairu, 2024, min samu karbar bakuncin muhimman baki, da suka zo daga ainihin Jiha ta kuma na farko domin ziyara a ofishinsa. Ina matukar farin ciki kwarai da wannan karramawar da aka yi Mani, ya mai girma Gwamna.

 

 

 

” Hakika mutane da dama za su yi mamaki kwarai matuka idan na ce masu Gwamna na da kuma minista duk suna taimaka Mani wajen neman wannan kujera ta shugabancin majalisar wakilai kuma taimakon tun daga ranar farko ne ake yin ta. Kuma za a yi mamaki kwarai idan na fara gaya wa jama’a cewa tunanin in fara yin wannan takarar ma duk ya fara ne da wadannan mutanen guda biyu da kuma babban yaya na tsohon Gwamnan Jihar Kaduna (El-rufa’i) su duka uku tare da ni aka fara wannan neman kujerar shugaban majalisa.

 

 

“Wasu mutane za su yi mamaki domin za a rika jin maganganu daban daban a kafafen yada labarai cewa wai Gwamna baya son shugaban majalisar wakilai ya fito daga Jiharsa; wato ni, kenan, domin wai ba tare muke ba a harkar siyasa. Saboda haka wannan ziyarar za ta nuna a fili cewa sai dai in akwai wadansu shugabannin majalisar wakilai da na su tare da Gwamnoninsu, don haka wannan ne na farko da zai zama abin misali ga wadansu suyi koyi”.

 

Shugaban majalisar ya kara da cewa shi da gwamna  Uba Sani suna tare kuma suna tattauna matsalolin da suke nan”, sai ya kara da cewa hakika suna nan tare har ko da aka samu shugabancin majalisar wakilan.

 

 

 

” Ba wani abin da zai iya tsaya mana a tsakanin mu har ya samu dakile sadarwa, hadin kai, kyakyawar dangantaka a tsakani, a matsayina na shugaban majalisa da Gwamnan Jihar Kaduna. Mu duk yan uwan Juna ne kuma zamu ci gaba da kasancewa hakan”, inji shi.

 

 

Da yake jawabi a game da batun Gwamna Sani da ya yi tun da farko na samun cikakken hadin kai musamman a bangaren jam’iyyun siyasa, sai shugaban majalisa Abbas, ya ce ” Gaskiya ne”. Ya kara da cewa ” ina a majalisar nan a tsawon wani lokaci, ba ta ba samun mutane masu hadin kai da kuma taimakawa Juna ba kamar wadannan da suke bayar da hadin kai ga shugabancin majalisa, wadannan mambobin majalisa ta 10″.

 

 

Ya kara jadda cewa mambobin majalisar sun bayyana goyon bayansu a fili a ranar 13 ga watan Yuni, 2023, a lokacin da aka Rantsar da majalisar ta 10 inda yan majalisa dari 353 daga cikin yan majalisa 359 da suke a majalisar a lokacin suka zabe shi ya zama shugaban majalisa. Kuma tun daga lokacin suke bashi duk wani hadin kai da ake bukata.

 

 

” Abu mafi muhimmanci, da zan gaya maku shi ne mambobin da suka fito daga Jihar Kaduna hakika suna ba ni cikakken hadin kai da goyon baya shi ya sa ma ko shi shugaban wannan yan majalisar ( Honarabul Amos Gwamna Magaji) da ya kasance daga yankin Kudancin Kaduna yake da kuma wata jam’iyya ta da ban ba APC, wato PDP  ba yana nan a halin yanzu saboda shi shugabanci na dukkan yan Najeriya ne ba tare da nuna bambancin siyasa ba. Sai dai tun da farko Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya shaidawa jama’a cewa wannan ziyarar a madadin dukkan al’ummar Jihar Kaduna ne baki daya”.

 

 

 

Ya kuma shaidawa taron jama’ar da suka hada da manyan jami’an majalisar da mambobi yan majalisa cewa, mutanen Jihar Kaduna suna alfahari da shugaban majalisar wakilai Abbas da kuma yadda yake gudanar da salon jagirancinsa.

 

 

 

 

” A matsayi na na tsohon dan majalisa na san irin wahalar da ke tattare da shugabancin majalisar wakilai. Amma a cikin tattaunawar da muka yi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da muka tattauna sau biyu ko uku ya shaida Mani cewa wannan majalisar ita ce ta fi kowace majalisa. Ya kuma fito fili ya bayyana Mani cewa a matsayinsa na tsohon dan majalisa, irin matsayin yadda ake tattaunawa a doron majalisar da yadda ake gabatar da kudiri da kuma samar da dokoki, suk idan an duba su sosai ana yi ne domin amfanin yan kasa, Najeriya.

 

 

 

” Kuma shugaban kasa ya shaida Mani cewa a duk lokacin da ya tattauna wani lamari da shugaban majalisar wakilai, hakika ya na samun sauki sosai idan ya kaiwa yan majalisa domin shugaban majalisa Abbas Tajudeen Tajudeen samun sauki wajen shawo kan yan majalisar. Domin kamar yadda muke gani tsakanin yan majalisa na akwai dangantaka mai kyau tsakaninsu ba tare da nuna bambancin siyasa ko jam’iyya ba

 

 

 

 

Gwamna Uba Sani ya kuma bayyana jindadinsa da irin yadda yan majalisar wakilan karkashin jam’iyyar APC da kuma na yan adawa duk suka hada kansu a karkashin jagorancin Abbas Tajudeen.

 

 

Jam’iyyun adawa guda Bakwai ne suke da wakilcin yan majalisa a majalisar ta 10, kuma guda uku duk suna da wakilcin shugabanci a matsayin marasa rinjaye.

 

 

Wadanda suke a lokacin ziyarar sun hada da shugaban marasa rinjaye, Honarabul Kinsley Chinda, sai mataimakin shugaban mai tsawatarwa Honarabul George Ozodinobo, da kuma wadansu wakilai daga Jihar Kaduna, Oyo da Jihar Gombe.

About andiya

Check Also

KASUPDA Organizes Stakeholders Engagement Programme

Community in the approved regularization layouts areas in Kaduna Metropolis have been advised to co- …

Leave a Reply

Your email address will not be published.