Home / Labarai / Ta’addanci: Mutanen Kasar Zazzau Sun Yi Zanga Zanga Zuwa Fadar Sarkin Zazzau

Ta’addanci: Mutanen Kasar Zazzau Sun Yi Zanga Zanga Zuwa Fadar Sarkin Zazzau

Daga Imrana Abdullahi
Wadansu mutanen da ke zaune a garin Tumburku a mazabar Kidandan a karamar hukumar Giwa cikin Jihar Kaduna a ranar Talata, 16, ga satan Janairu, sun yi Zanga zangar nuna bacin ransu sakamakon matsalar rashin tsaron da ta yi masu katutu har ta zamanto ba su iya yin Noma domin samun abinci da kuma ciyar da kasa baki daya.
Hakika matsalar tsaro na addabar mu kwarai lamarin kuma sai karuwa yake yi Dare da rana.
Jagoran masu Zanga Zangar, Malam Yusuf Jibrin cewa ya yi suna cikin damuwar kwarai Dare da rana sakamakon matsalar yan Ta’adda da ke addabar jama’ar yankin, wanda sakamakon hakan harkokin Noma sun samu nakasu kwarai.
Masu Zanga zangar sun kuma ce yan ta’addan na sata da kuma kashe mutane a duk lokacin da suka ga dama saboda haka ba su bari ayi Noma har sai an biya kudin fansa ko diyyar da suka Sanya.
Wani mutum mai suna Aminu Abubakar mazaunin Tumburku cewa ya yi mafi akasarin jama’a a kauyuka ba su da abincin da za su ci, saboda haka ne suka kawo kukansu ga mai martaba domin a dauki mataki.
Da yake mayar da jawabi mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli cewa ya yi mai Unguwar Kauyen Kidadan na bayar da rahoton faruwar irin yadda lamarin ke faruwamara dadi ga masarautar.
“Wanda hakan ya Sanya irin yadda matsalar take a karamar hukumar Giwa na haifar mana da rashin yin bacci”.

About andiya

Check Also

Northern govs meet in Kaduna, design regional economy, human capacity devt

    The chairman, Northern States Governors’ Forum (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, has called for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.