Gwamna Dokta Dikko Umaru Radda na Jihar Katsina ya rusa duk wasu wadanda aka nada mukamai na siyasa a jihar nan take ba da bata lokaci ba.
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Ahmed Musa Dangiwa ne ya fitar da sanarwar, da ta ce don haka gwamnan ya umarci duk masu rike da mukaman siyasa da su mika ayyukan ofisoshinsu ga babban darakta a dukkan hukumomi ko bangarorin Gwamnati da suke yi wa aiki.
Sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Musa Dangiwa. ya ce duk da haka, umarnin ya kebe hukumar jin dadin alhazai ta jihar da za ta ci gaba da zama a kwamitin har sai an kammala aikin Hajjin 2023.
“Mai Girma, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana godiya ga wadanda aka nada saboda gudunmawar da suke bayarwa ga Jihar Katsina,” in ji Ahmed Musa Dangiwa.