Home / Labarai / Gwamnan Matawalle Zai Kawo Karshen Cin Zarafin Yara

Gwamnan Matawalle Zai Kawo Karshen Cin Zarafin Yara

Takardar Manema Labarai

GWAMNAN MATAWALLE  YA HIMMATU DOMIN KAWO KARSHEN WULAKANTA YARA DA SAFARAR MUTANE TAHANYAR TATTAUNAWA DA MALAMAN ADDININ ISLAMA DA SHUGABANNI, SARAKUNAN GARGAJIYA A JIHAR.

Mai Daraja, Gwamnan Jihar Zamfara Honarabul Dokta. Bello Mohammaed MON ( Matawallen Maradun) ya ce Gwamnatinsa na kokarin ganin bayan dukkan wani nau’in bata yara da wulakantasu tare da safarar mutane a cikin Jihar ta hanyar tattaunawa fitattun Malaman addinin Islama da kuma sarakunan Gargajiya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau a wurin taron jin ra’ayin jama’a bisa bukatar kakkabe matsalar wulakanta yara da kuma safararsu ta hanyar samar da tsarin ingantaccen ilimi mai nagarta taron dai an yi shi ne a Majalisar kasa inda ake yin doka  da ke Abuja.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishiniyar kula da harkokin mata, yara da bunkasa harkokin ci gaban jama’a, Hajiya Zainab Lawal Gumi ta ce Gwamnatin Jihar Zamfara a shirye take domin ganin bayan duk wani nau’in wulakantar da yara da suka hada da Sanya yara aikin da ya fi karfinsu, wulakantar da su tare da safarar mutane ta hanyar yin amfani da malaman addinin musulunci da sarakunan gargajiya domin a samu hanyoyi da basirar da za a iya magance matsalar ta hanyar samun ingantattun dokoki a Jihar.

Ya ce tuni an samar da kwamiti da Gwamnatin Jihar ta kafa da za su duba batun bambancin tsakanin al’umma da rikice rikice da wulakanta yara wanda za a kaddamar nan gaba kadan.

Gwamnan ya ci gaba da cewa akwai wani kudiri a kan batun yancin yara a gaban majalisar Jiha tuni har ya wuce karatu na daya wanda idan an mayar da shi doka zai mayar da ilimi ya zama dole ga dukkan yara masu kananan shekaru a Jihar.

Matawalle ya kuma ja hankalin yan majalisar a bisa bukatar da ake akwai ga shirin Gwamnatin tarayya domin kawo Tallafi musamman ganin irin dimbin marayu da Jihar ke da su sakamakon irin shekarun da aka samu da matsalar yan bindiga da lamarin ya haifar da dimbin marayu da yawa.

Ya bayyana cewa Gwamnatinsa ta kirkiri tsare tsaren taimakawa mutane da niyyar samawa jama’a sauki daga cikin mawuyacin halin da suke ciki wanda sakamakon hakan zai taimakawa yara a Jihar.

Da yake bayanin bude taron, shugaban majalisar tarayya ta kasa, Femi Gbajabiamila ya yi tulawar baya inda ya fayyace cewa batun yancin yara an Sanya shi a matsayin doka wanda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shekatu 17 da suka gabata a shekaru 2003 amma a halin yanzu jihohi da yawa har yanzu ba su samar da dokar ba dokar dai za ta kare yancin yara ne a jihohi.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa batun samar da yancin yaran zai tabbatar da ganin kare yancin yara domin samar da rayuwa mai inganci domin samun ilimi ga dukkan yara tun a matakin karatun Firamare da karamar Sakandare a kasa baki daya kuma dokar za ta samar da wani hukunci ga iyayen da suka kasa yin aiki da dokar kamar yadda ya dace.

Ya kuma yi kira ga dukkan mahalarta taron a wajen jin ra’ayin jama’ar da su kula da batun samar da yancin yaran a matsayin lamarin da ke bukatar taimakon kowa domin taimakawa.

A lokacin taron jin za a yin jama’ar an samu tofa albarkacin baki daga jihohi da dama, masu yi wa kasa hidima, hukumar kididdiga ta kasa, ma’aikatar aikin Gona da bunkasa karkara, hukumar da ke yaki da safarar bil’adama, hukumar ilimin bai daya ta kasa UBE da dai sauransu.

Mutanen da suka samu halartar taron daga Jihar Zamfara sun hada da mataimakin shugaban ma’aikatan gidan Gwamnati, Dokta Bashir Muhammad Maru, kwamishinan ayyukan musamman, Honarabul Muhammad Maiturare Sadiq, babban sakataren Gwamnan na kashin kansa Lawal Umar Maradun da Darakta Janar a kan harkokin kafafen yada labarai da wayar da kan jama’a da sadarwa, Malam Yusuf Idris Gusau.

YUSUF IDRIS GUSAU

Darakta Janar kan harkokin kafafen yada labarai da wayar da kan jama’a tare da sadarwa na Gwamnan Jihar Zamfara a gidan Gwamnatin Jihar da ke Gusau.

03 Nuwamba, 2020

 

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.