Daga Imrana Abdullahi
Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya amince da Rusa wasu hukumomi da Ma’aikatun Gwamnatin Jihar.
Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar Abubakar Usman ya fitar a ranar Litinin, ta kuma sanar da soke duk wasu nade-naden siyasa da aka yi kafin ranar 29 ga Mayu, 2023.
A cewar sanarwar, rushewar ta hada da na ka’ida da na hukumar da ba na doka ba
A yayin da Sakataren Gwamnatin ya yaba da irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar da kuma harkokin ofishinsu.
Sanarwar ta kuma umarci hukumomin da abin ya shafa da su mika dukkan kadarorin gwamnati da suka hada da motocin hukuma da ke hannunsu ga babban Daraktan da ke hukumar da suke aiki .