Home / Uncategorized / GWAMNAN ZAMFARA YA YI TA’AZIYYAR RASUWAR ƊAN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR, HON. AMINU K/DAJI

GWAMNAN ZAMFARA YA YI TA’AZIYYAR RASUWAR ƊAN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR, HON. AMINU K/DAJI

 

 

 

 

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu.

 

 

 

Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.

 

 

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyar sa ga Majalisar Dokokin jihar da Iyalan mamacin.

 

 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta aika da tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Mani Mummuni a yayin jana’izar ta marigayi Aminu K/Daji in Kauran Namoda.

 

 

 

“A madadin gwamnatin jiha,muna miƙa saƙon ta’aziyyar mu ga shugaban Majalisar Dokokin, sauran shugabanni a Majalisar, iyalai da al’ummar Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda ta Kudu.

“Muna kuma yin addu’a Allah ƙara ma iyalai jimirin jure wannan rashi. Muna kuma addu’ar Allah gafarta wa marigayin kurakuran sa.

About andiya

Check Also

Dangote Supports FCT, Kogi In N16bn Food Programme

……FCT Minister, Kogi Gov applaud ADF   The Federal Capital Territory(FCT) Abuja and the Kogi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.