Home / Labarai / Gwamnatin Jihar Neja Ta Haramta Dukkan Wata Zanga Zanga

Gwamnatin Jihar Neja Ta Haramta Dukkan Wata Zanga Zanga

Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da cewa ta hana dukkan wata nau’in Zanga Zanga a fadin Jihar baki daya.
 Bayanin hakan ma kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun jami’in yada labarai a ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Lawal Tanko da aka rabawa manema labarai da takardar ta tabbatar da cewa hanin ya fara aiki ne nan take.
Sanarwar ta kuma ce ta haramta dukkan wani taron gangami a kan taron Maulidi, gangami da duk wani taron jama’a mai yawa a kan tituna da zai iya toshe titin a duk fadin Jihar Baki daya.
Sakataren Gwamnatin Jihar Ahmed Matane ya kuma taya musulmi murnar bikin zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammadu SAW, inda ya ce ana shaidawa kowa ya yi bikin a inda yake
Ya ci gaba da cewa wannan matakin na yin hani game da duk wani gangamin jama’a ya samo asali ne sakamakon irin matsalar tsaron da ake fama da shi a kasa wanda ya samo asali daga gangamin kawo karshen jami’an Yan Sanda na SARS.
Sakataren Gwamnatin ta ce duk da Gwamnatin za ta ci gaba da mutants yancin kowa na yin al’amuran na yau da kullum, kuma Gwamnatin ba za ta zuba idanu ba tana kallon ana kokarin take yancin da wasu suke da shi da zai kai ga karya doka da oda a cikin al’umma da kuma a kan titunan Jihar ba.

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.