Home / News / Da Shaikh Jafar Da Albani Zariya Suna Da Rai Da Wani Cewa Zai Yi Kudi Aka Ba Su – Gwamnan Yobe

Da Shaikh Jafar Da Albani Zariya Suna Da Rai Da Wani Cewa Zai Yi Kudi Aka Ba Su – Gwamnan Yobe

Da Shaikh Jafar Da Albani Zariya Suna Da Rai Da Wani Cewa Zai Yi Kudi Aka Ba Su – Gwamnan Yobe

Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, ya bayyana cewa kamar yadda malamai biyu suka bayyana wa jama’a cewa idan Buhari ya hau karagar mulki wani cewa zai yi an ba su kudi ne suka fadi abin da suka fadi a baya kafin Buhari ya hau mulki.
Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewa kamar yadda shaihunnan Malaman biyu suka bayyana cewa jama’a za su yi ta addu’a, Azumi da alkunutu domin Buhari ya hau kan mulki.
“Amma malaman sun ci gaba da cewa idan Buhari ya hau mulkin ko shi ba zai san irin zurfin barnar da aka yi wa kasar ba sai ya hau tukuna, kuma zai yi kokarin samar da gyara amma za a sha wahala kafin gyaran ya tabbata”.
To da suna da rai da wani cewa zai yi kudi aka ba su domin gaskiyar da suka fadi.
Mai Mala Buni ya kara da cewa idan ba Nijeriya ba ta yaya kasar da aka Barbara da makudan kudi irin dala biliyan sha shida za ta zauna da kanta bata rushe ba, ai sai a godewa Allah.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta bbc hausa, inda ya kara da yin kira da cewa ya dace masu kokarin sai fitina ta tashi a kasar nan su Sani sai da akwai kasar sannan komai zai wakana, don haka kowa ya yi hankali musamman shugabanni.
“Shugabannin ai ko masu Unguwanni ma shugabanni ne da sauran dukkan masu shugabantar jama’a kowa ya shiga hankalinsa domin a samu ci gaban kasa baki daya”.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.