Home / Labarai / Gwamnatin Jihar Sakkwato Ta Amince Da Sabon Albashi

Gwamnatin Jihar Sakkwato Ta Amince Da Sabon Albashi

Imrana Abdullahi

Gwamnantin Jihar Sakkwato ta amince da aiwatar da batun sabon tsarin albashin ma’aikatan Jihar.

Kwamishinan yada labarai na Jihar Sakkwato, Isah Bajini Galadanci ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a dakin taro na Gidan Gwamnatin Jihar Sakkwato.

Ya ce majalisar zartaswa ta Jihar tuni ta amince da dukkan abin da aka tattauna kuma aka zartar a karkashin kwamitin da Gwamnatin ta kafa domin duba yadda batun karin albashin zai kasance.

Alhaji Isa ya kuma yi bayanin cewa Karin albashin zai fara aiki ne a karshen watan Janairu 2020.

Da yake jawabi shugaban ma’aikatan Jihar Alhaji Buhari Bello Kware, cewa ya yi an amince da a biya naira dubu 30 ha ma’aikatan da suke matakin albashi na 1 zuwa na 6 sai kuma wadanda ke matakin albashi na 7 zuwa na 8 za a kara masu bashi 22 colin dari wadanda suke matakin albashi na 9 zuwa na 10 aa su samu karin bashi 17 ne a cikin dari.

Kware, ya kara da cewa masu matakin albashi na 12 zuwa 14 kuma za su samu karin bashi 12 colin dari sai kuma masu mataki na 15 aa su samu karin kashi 9 cikin dari.

Shugaban ma’aikatan ya kuma yi amfani da wannan dama inda ya godewa Gwamnan a kan wannan karin albashin da ya yi wa ma’aikata ya kuma yi kira ga ma aikatan da su saka abin da aka yi masu da alkairi ta hanyar yin aikin bisa adalci da gaskiya.

Daga cikin kwamishinonin da suka halarci wajen ganawa da manema labaran sun hada da kwamishinan kudi Abdussamad Dasuki sai kuma na walwala da jin dadin jama’a Furofesa Hajiya A’ishatu Madawaki Isa.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.