Home / Labarai / Gwamnatin Kaduna Ta Hana Aiki Da Babura Mai Kafa 2 Da Mai Kafa uku

Gwamnatin Kaduna Ta Hana Aiki Da Babura Mai Kafa 2 Da Mai Kafa uku

Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ta sanar da hana yin aiki da Mashina masu kafa biyu da yar kurkura mai kafa uku saboda tsoron yaduwar cutar Korona Bairus.
Gwamnatin Jihar kaduna sun bayyana daukar matakin ne da suka ce masu haya da Baburan ba za su iya daukar matakin samar da tazara ba tsakanin masu amfani da shi.
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna Dakta Hadiza Balarabe ce ta sanar da hakan a wata sanarwa ta kafafen yada labarai a ranar Laraba, tana mai cewa an dauki wannan matakin ne bayan wani kwamitin da aka kafa domin ganin irin yadda mutane suka bayan da hadin kai da goyon baya game da matakan da aka dauka domin yaki da cutar Covid 19 da ake kira  Korona Bairus.
Mataimakiyar Gwamnan ta ce motocin jigilar Jama’a na Bus an amince da su ci gaba da aiki ya zuwa yanzu amma su tabbatar sun kiyaye ka’idar da aka Sanya masu na daukar mutane biyu biyu a kowace kujera da ke tsakiyar motar da kuma kujerar baya.
Kamar yadda ta bayyana cewa Gwamnati a shirye take domin Dakatar da kowane irin taron Jama’a da zai iya haifar da yada wannan cuta ta Korona.
Ta kuma bayyana cewa tuni aka fara biyar Albashin wannan watan inda ta yi kira ga dukkan wanda ya samu albashin nasa da ya yi amfani da shi da lura kasancewar irin halin da aka shiga a halin yanzu.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.