Home / News / Gwamnonin PDP Za Su Hada Hannu Da Al’ummar Duniya Domin Inganta Dimokuradiyya

Gwamnonin PDP Za Su Hada Hannu Da Al’ummar Duniya Domin Inganta Dimokuradiyya

Imrana Abdullahi
A kokarin ganin an kara inganta harkokin Dimokuradiyya a Nijeriya Gwamnonin Jam’iyyar PDP na kokarin hada Gwiwa da al’ummar duniya domin ganin kwalliya da cimma kudin sabulu
Tuni dai Gwamnonin jam’iyyar PDP ta karkashin shugaban kungiyar ta su Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal suka fara tattaunawa da wadansu al’ummar duniya domin aikin inga ta Dimokuradiyya ta yadda kowa zai amfana
 Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da hadin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a kan harkokin yada labarai Muhammad Bello ya Sanya wa hannu.
Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, wanda shi ne sabon shugaban kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP ya tattauna da Jakadan kungiyar tarayyar Turai Ketil Karlsen da kuma Mary Beth Leonard a garin Abuja.
 Tattaunawar dai an yi ta ne a kan batun samar da ingantaccen ci gaba a Nijeriya da irin gudunmawar kungiyar Gwamnaonin PDP domin ciyar da harkokin Dimokuradiyya gaba, musamman ta fuskar samar da ingantattun cibiyoyin Gwamnati da tsarin mulki tare da samar da tsare tsaren gudanar da harkokin zabe da kuma samar da ingantaccen shugabanci.
Dukkan bangarorin da suka halarci taron sun tattauna a kan basira da tsare tsaren kasa da kuma na gudunmawar kasashen waje a kan yadda za su samu hadin kai tsakanin bangarorin da kuma J9hohin da PDP ke jagoranta a game da wadansu fannoni da ke bukatar dauki.

About andiya

Check Also

Sultan urges muslims, Nigerians to reconcile selves for peace, unity says ‘don’t allow politics  divide you’

By Suleiman Adamu, Sokoto Ahead of the Ramadan fast around the corner, the Sultan of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.