Home / Big News / Gyaran Matsalar Najeriya Ba Na Mutum Daya Bane

Gyaran Matsalar Najeriya Ba Na Mutum Daya Bane

 

Shugaban jam’iyyar PDP mai jiran gado, Sanata Iyorchia Ayu ya baiyana cewar, aikin gyaran matsalar Najeriya ta fi karfin mutum daya ko wani bangare, dole ne a taru a hada kai domin  ceto Najeriya daga wargajewa  a sakamakon mulkin ganin dama daa rashin tabbas na jam’iyyar APC da ya janyo koma baya da rashin ci gaba.

 

 

Sanata Iyorchia Ayu ya fadi haka a taron da yayi da yan jarida a Abuja bayan kammala taron bita da ilmantar da sabbabin shugabanin jam’iyyar PDP da akayi na kwanaki biyu da suka gabata.

 

 

Shugaban mai jiran gado ya amince da cewar, a baya PDP ta tabka kura-kurai wanda ya sanya yanzu ta falka don ganin ta ceto Najeriya da yan Najeriya daga wadanan matsalolin da suke ciki.
Yace, shugabani nada muhimiyyar rawa da ya dace su taka ga ganin an tayar da komadar kasarnan da sake mata fasali ganin yadda Shugaban Kasa Buhari yake kokarin mayar da ita a matsayin mabaraciya da rashin makoma da haddasa rarrabuwa kawuna a tsakanin yan kasa.

 

” Najeriya ta zama juji na matsaloli da kuma komawa tamkar mabaraciya duk da arziki da damar da Allah Ya huwace mana, sakamakon irin Mulkin kama karya da na rashin hikima wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar sa ta APC suka haddasa”
Inji Iyorchia Ayu.

 

 

 

Makomar Najeriya anan gaba

Haka ma yace’ aikin mu a matsayin Shugabani Jam’iyyar PDP a yanzu yana da matukar samun hadin kai, fatan alheri da kuma gaskiya don ceto kasarnan daga mummunan yanayi na rashin tabbas, kalubale da barazana tsaro da sauran ababen dake iya janyo lallacewa kasarmu baki daya.

 

 

“Kowane dan Najeriya yana da kyau ya mayar da hankali ga abin da zai amfanar da kasa a maimakon kara haddasa matsala da zata wargaza hadin kai da ci gaban mu” Inji Sanata Ayu

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.