Home / Labarai / Harin Matasan Oyo Kan Al’ummar Fulani: Wata Alamar Aika Sako Mara Kyau Ce Ga Kasa Baki Daya – Kungiyar ACSC

Harin Matasan Oyo Kan Al’ummar Fulani: Wata Alamar Aika Sako Mara Kyau Ce Ga Kasa Baki Daya – Kungiyar ACSC

Harin Matasan Oyo Kan Al’ummar Fulani: Wata Alamar Aika Sako Mara Kyau Ce Ga Kasa Baki Daya – Kungiyar ACSC

 

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

 

KUNGIYAR Arewa Consultative Synergy Congress (ACSC), ta bayyana harin da wasu matasa suka kaiwa wasu Fulani makiyaya a jihar Oyo a matsayin wani aiki na dabbanci da ke aikawa kasar wata sako mara kyau da bai dace ba,

 

 

Da yake jawabi a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban Kungiyar ta kasa Dakta Engr, Harris HM Jibril, ACSC ta bayyana cewa lamarin na baya-bayan nan wata alama ce ta barazana ga al’umma duba da yin la’akari da irin kyakkyawar alakar dake tsakanin Yarbawa da Hausa Fulani a kasar.

 

 

Sanarwar ta kara da cewa, harin na baya-bayan nan ya kasance abin tayar da hankali da takaici domin kuwa karya ce ta firgita matasa don su mamaye garuruwan Fulani makiyaya da ke yankinsu.

 

 

A cewarsu, irin wannan aikin na iya zama wata barazana ga zaman lafiyar kasar da ake ta wahala ba dare ba rana don kiyayewa da kuma samun damar haifar da martanin da ba za a iya kaucewa ba daga wasu sassan kasar.

 

 

Hakazalika, kungiyar ACS_Congress ta yi Allah wadai da irin wannan ayyukan da ke bayyane na nuna bambancin kabila da kabilanci tare da yin kira ga gwamnati da ta hanzarta wajen maido da zaman lafiya da oda a cikin al’ummomin da abin ya shafa domin ta hanyar zaman lafiya ne kawai ci gaban zai iya dorewa.

 

 

A karshe, kungiyar ACSC ta yi kira ga matasan Arewa da su guji daukar mataki a hannunsu kada su bari tunanin daukar fansa ya rude su da labaran karya ta hanyar sanyawa a cikin zukatansu domin hakan na iya gurbata zaman lafiyar da suke rike da ita.

 

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.