Home / News / HARUNA A G YA KOMA GIDA PDP A KADUNA

HARUNA A G YA KOMA GIDA PDP A KADUNA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Tsohon babban akanta Janar na Jihar Kaduna da ya fi kowane akanta Janar dadewa a kan mukamin Alhaji Dokta Haruna Yunusa Sa’id Kajuru, ya bayyana cancanta, kokari, iya aiki da sanin ciki da wajen Jihar a matsayin ma’aunin da za a yi amfani da shi a zabe shi Gwamnan Jihar.
Haruna Yunusa Kajuru ya bayyana hakan ne a lokacin wani gangamin dawowarsa gida da kuma bayyana wa yayan PDP cewa ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Kaduna a sakatariyar jam’iyyar da ke NDA Kaduna.
Haruna Yunusa A G ya ce ” kamar yadda ya Sani shi ne a kan gaba wajen ganin jam’iyyar APC ta Kafu sosai a Jihar Kaduna, har aka samu nasarar da ake takama da ita a yanzu amma kuma bisa wadansu dalilai a halin yanzu ya koma asalin gidansa na PDP wanda aka kafa ta da shi ya kuma rike mukamai tare da yin ayyukan ci gaban rayuwar jama’a da dama”.
Ya kara da cewa ” ni ne ma’aikacin da ya fi kowa dadewa a kan kujerar babban akanta Janar a Jihar Kaduna domin na shekara Goma sha daya (11) da ba a ta ba samun wanda ya samu damar yin hakan ba, na kuma yi aikin karantarwa tun daga Firamare, sakandare zuwa jami’a na yi aikace aikace da dama da suka hada da shugaban kamfanin zuba jari da hukumar NAITI inda na zama shugaba baki daya a Najeriya”.
Haruna Kajuru ya ce ni ne dai wanda aka Sani ina nan ban canza ba sai ci gaban da na yi, kuma na gina makarantar sakandare tun daga matakin aji uku zuwa babbar sakandare na ba Gwamnati kyauta na kuma gina makarantun Islamiyya da masallatai duk domin taimakawa bayin Allah.
A G Kajuru ya ce ko a halin yanzu da akwai abubuwa da dama da zan yi wa Jihar Kaduna domin a samu ci gaban da kowa ke bukatar samu.
” Sai dai ya koka da irin yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ke aikin tituna a garin Kaduna da kuma yan kadan a Zariya da Kafanchan wanda ya ce hakika hakan da sauran abin dubawa domin kamar shi da ya fito daga kauye har yanzu su na jiran ayi masu aiki, na kuma san Jihar Kaduna kwarai domin tun daga Gwantu zuwa Fala zuwa yankin Dogon Dawa har karshen birnin Gwari a Jihar Kaduna duk ko’ina mun san haka, balantana kuma wanda ya yi aiki a makogwaron Jihar Kaduna ta fuskar kudi saboda duk kowace ma’aikata sai ta zo ofishin akanta Janar na kuma yi aiki shekaru Goma sha 11.
A nasa jawabin shugaban jam’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna Honarabul Felix Hassan Hyat, cewa ya yi babu wani dan takarar da za su dannewa hakki su kowa na su ne don haka sai wanda jama’a kawai suka ce su na so a dukkan wadanda za su tsaya takara a jam’iyyar.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.