Home / Labarai / Hassada, Kiyayya Da Gaba A Tsakanin Malamai Ya Yi Yawa- Dokta Hamisu Ya’u

Hassada, Kiyayya Da Gaba A Tsakanin Malamai Ya Yi Yawa- Dokta Hamisu Ya’u

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
USTAZ DOKTA HAMISU YA’U, sanannen Malami ne mai wa’azin addinin musulunci kuma dan kasuwa ya bayyana cewa akwai wadansu matsalolin da suka yi wa jama’a yawa musamman ma kuma a bangaren malamai.
Dokta Hamisu Ya’u, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wa’azin watan Ramadana a masallacin ‘Chice plaza’ da ke kan titin Alkali a Kaduna.
Dokta Hamisu Ya’u ya ce babbar matsalar malamai a halin da ake ciki ita ce hassada, kiyayya da ganin kyashin Juna, wanda sakamakon hakan ya sa hatta yan siyasa ke yi wa malamai yadda suka ga dama.
Dokta Hamisu Ya’u, ya ci gaba da cewa lamari ne da ke tattare da gudanar da rayuwar jama’a inda batun fadin karya kiri kiri ya zama wani al’amari ne da Yan kasuwa ke yin riko da shi.
A bangaren Mata kuma suke rungumar yin Ha Inci ya zamar masu wani abin yi da za su iya aikatawa kowa a cikin al’umma, wanda sanadiyyar wadannan abubuwan da ke cikin al’umma sai lamarin ya zama wata gagarumar matsalar da ke addabar kusan dukkannin sunita baki daya.
Hassada da shedan ya buga ganga sai malamai suka ce a barmasu kayansu ne
A halin yanzu iyaye mata suna matukar murna da farin ciki idan sun haifi da Namiji domin ya samu Gadon Dukiya mai yawa tsakaninsa da yaya mata.
“Batun tara makudan kudi ya zamar wa jama’a fitina, yan kasuwa da malamai duk sun mayar da hankalin su kudi kawai,zaka ga Malami ya sa yi mota burinsa ya zama ba kamar shi ya dai Sanya Agogo mai tsada kawai”.
Ga kuma matsalar neman cin gadon Dukiya musamman ga mata masu zaman auren jiran cin Gado ba zaman aure kamar yadda musulunci ya bayyana ba, “mun samu labarin cewa wasu masu kudi yan kasuwa ba su cin abincin gidansu domin gudun kada a Sanya masa wani abu ya ci ya mutu”.
Halin da ake ciki shi ne mutum daya a duniya ke fatan ace ya fi shi kudi, Uba ne ke son dansa ya fi shi kudi,amma kuma Uba baya son dansa ya fi shi mulki ba.
“Mutane na bacewa baki daya domin su samu kudi, wata rana wani boka ya Sanya masa sharadin yin zina da uwarsa ya kawo maniyin uwar ayi aiki, da kuma wanda aka ba shi sharadin ya kawo wa boka yin wanka da jinin dan da ya fi so kuma haka aka yi, sai wanda ya kashe uwarsa ya kawo wa boka farjin uwarsa da ya yanke daga jikinta bayan kashe ta, wannan fa har yan Sanda sun kama shi lokacin da ya dauki farjin da ya yanke a jikin uwarsa, to jama’a mu dubi halin da muke ciki fa”, inji Ustaz Hamisu Ya’u.
“Ko makiyin ka baka fatan ya shiga cikin hannun wadannan mutane domin kazantarsa ya yi yawa, kuma wannan masifa ce domin kawai a samu kudi a nan duniya, don haka lokaci ya yi da kowa zai duba kansa shin meye laifinsa a wajen Allah domin a gyara”.
Ga kuma wata fitina ta mata a cikin gida ga kuma ta yaya
Da kuma matsalar mata a waje bayan mutum ya fito daga cikin gida
“Wata fitinar ta fito wato a dandalin Sada zumunta na tiktok, inda mata ke tallar kawunansu, har wasu ma zaka gansu kamar tsirara, saboda haka harkar mata fitina ce a karshen zamani sai dai fatan Allah ya kiyaye mu baki daya”.
Sai kuma fitinar sabawa iyaye duk da Allah ya ce a kyautata, abi iyaye a kyautata masu domin wajibi ne, amma abin da ke faruwa a yanzu iyaye na cikin tsaka mai wuya,saboda iyaye ne ke kyautata wa yayansu ba su yayan ke kyautata wa iyaye ba”.
Malam Wanda ya kasance Malamin jami’a ne Dokta Hamisu Ya’u, ya bayyana hakkin Uwa da Uba da cewa Uba na da cikakken hakkin mallakar dan da suka haifa, ita kuma uwa wajen tausayawa don haka a rika kokarin kiyaye wadannan abubuwa ba kamar yadda aka Dora jama’a ba sanadiyyar hadisin da ya gabata wanda ya nuna uwa farko har sau uku.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.