Home / Labarai / Hatsarin Jirgin ruwa: Kakakin Majalisar Abbas ya yi alhinin wadanda abin ya shafa, ya nemi matakan kariya

Hatsarin Jirgin ruwa: Kakakin Majalisar Abbas ya yi alhinin wadanda abin ya shafa, ya nemi matakan kariya

Daga Imrana Abdullahi

Kakakin majalisar wakilai Honarabul  Abbas Tajudeen ya bayyana Alhini da bakin cikinsa dangane da hadurran kwale-kwale da aka yi a kasar a baya-bayan nan, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Wata sanarwa da Musa Abdullahi Krishi, mashawarci na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban majalisar ya fitar, wadda aka rabawa manema labarai, ta ce lamarin ya faru ne a jihohin Adamawa da Neja.

Kakakin majalisar Abbas ya yi kira da a hada kai da gwamnati da ma’aikatan jirgin domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya a kan hanyoyin ruwa.

A daren Juma’ar da ta gabata, an ce mutane da dama sun mutu bayan da wani jirgin ruwa ya kife a tafkin Njuwa, kauyen Rugange a karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji sama da 100 a karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja ya kife, inda fasinjoji 30 suka mutu.

A ranar Litinin kuma, an samu rahoton wani hatsarin kwale-kwale a garin Kwatan Mallam Adamu, da ke kauyen Gurin, a karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, inda ya halaka mutane sama da 10.

Shugaban majalisar ya yi Allah wadai da halin da harkar sufurin ruwa da ke zaman madadin hanya da jirgin kasa domin yin zirga-zirgar jama’a da kayayyaki, a halin yanzu ke ta tafka barna.

Kakakin majalisar Abbas, ya bukaci hukumomin da abin ya shafa da su yi la’akari da sake duba ka’idojin gudanar da aiki, tare da neman a bi duk matakan kariya daga ma’aikatan jirgin da fasinjoji.

Shugaban majalisar yayin da yake addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu, ya kuma jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa, da jama’a, da gwamnatin jihohin Neja da Adamawa kan wannan lamari da ya shafa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.