Related Articles
Honarabul Abubakar Yahya Kusada Ya Gabatar Da Kudirori 3 Gaban Majalisar Wakilai
Injiniyan Zanen taswirar Gine Gine tare da kididdiga Honarabul Abubakar Yahya Kusada mniqs, CIPA, dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kankiya,Ingawa da Kusada a majalisar wakilai ta tarayya ya gabatar da kudirori uku gaban majalisar yana bukatar su zama dokar kasa.
Kudiri na daya shi ne a kan inganta hukumar muhalli ta kasa mai lamba ( HB 1123 ) kamar yadda dan majalisa Abubakar Yahya Kusada ya gabatar ya tsallake karatu na farko.
Sai kudiri na biyu shi ne sake samar da ingantacciyar doka a game da hukumar kula da asibitoci mai lamba ( HB 1124 ) kamar yadda dan majalisa Abubakar Yahya Kusada ya gabatar kuma ita ma ta tsallake karatu na farko.
Sai kuma kokarin samar da doka a kan a game da hukumar makamashi ta kasa ita ma mai lamba ( HB 1125 ) kamar yadda dan majalisa Abubakar Yahya Kusada ya gabatar duk nan ma ta tsallake karatun farko a gaban majalisar dokokin tarayya.
Wadannan kudirori duk an gabatar da su a gaban majalisar wakilai ta tarayya a ranar Talata 1 ha watan Disamba, 2020 a lokacin zaman majalisar an kuma yi masu lamba kamar haka 10, 11 da 12 dukkansu sun tsallake karatun farko.