Home / News / MUN KARBI FADUWAR PDP DA MUTUNCI DA DATTAKO – GWAMNAN BAUCHI

MUN KARBI FADUWAR PDP DA MUTUNCI DA DATTAKO – GWAMNAN BAUCHI

 MUN KARBI FADUWAR PDP DA MUTUNCI DA DATTAKO – GWAMNAN BAUCHI
Jamilu Bauchi
: Yace rashin nasarar darasine garemu baki daya
Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na jihar Bauchi ya bayyana jindadinsa da Godiyarsa ga  daukancin mambobin PDP da goyon baya da yarda da rashin Nasara da aka yi a jam’iyyar PDP na zaben da yagudana na cike gurbi na Majalisar jiha a Dass mun karbi faduwar da mutunci da dattako.
Gwamnan yabayanna rashin samun nasarar jam’iyyar PDP a matsayin  haka Allah yaso, yakuma Kara karfafa gwiwa wa membobin jam’iyyar Kar wannan yasa asamu rarrabuwar kai da koma baya.
Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir yakuma bayyana rashin samun nasarar a matsayin darasi ne gamu duka da Gwamnati da jam’iyyar PDP munada bukatar yin tsare-tsare don rike Martaban jam’iyyar da hikimomi da dabarbaru da Kuma aiki a tare.
” Dukkan godiya yatabbata ga Allah. Rashin nasarar jam’iyyar mu tabbas darasine a garemu duka, Babu Kuma wadda zamuyi zargi akan haka.
” In zaku iya tunawa mun rasa kujeru 21 na Majalisar Dokoki da Sanatoti guda Uku a 2019 Amma Allah yabamu Sa’a mukaci zaben Gwamna. Kar mu zargi kowa a cikin Wanann al’amari, mubarshi a cikin gida, Banda cece kuce, da rashin yadda da Juna”
Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir yabayanna farin cikinsa ga duka membobin jam’iyyar PDP na bada goyon bayansu da Gudumawa na ganin an samu nasarar Gwamnatinsa.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.