Hukumar Tsara Birane da Samar da Cigaba ta Jihar Kaduna (KASUPDA) ta bayyana rashin jin dadin ta kan yadda a ka koma yin gine-gine ba tare da samun izini daga Hukumar ba.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun Nuhu Garba Dan’ayamaka, MNIPR, wanda shi ne jami’in hulda da jama’a na hukumar KASUPDA,da aka rabawa manema labarai a Kaduna.
Hukumar ta yi nuni,bisa dubi da nasarori da aka cimma wajan inganta tsarin birane da aiyukan sabunta tsarin birane da kuma kawata gari a Jihar Kaduna, ta bayyana rashin jin dadinta a kan wadan da suke yanke hukuncin yin gine-gine da kafa shaguna da rumfuna da kwantena-kwantena da kiyos- kiyos da
sauran allunan tallace-tallace ba tare da samun izini ba, a ya yin da masu tallace-tallace a gefen titina ke dawowa gadan-gadan wajan gudanar da harkokin kasuwancinsu a gefen titina da aka tashe su.
Dan haka, Hukumar na tunatar da jama’a cewa, KASUPDA ita ce ke da alhakin kula da tsarin birane a duk fadin Jihar Kaduna.
Ta wannan ne Hukumar KASUPDA ke kara jaddada kudirinta na gudanar da aiyukan da suka rataya a kan ta, domin tabbatarwa da kuma habaka tsarin birane, dan kare rayuka da batutuwan tsaro a Jihar mu.
Duk wanda ya ki bin ummarni da dokoki, Hukumar KASUPDA, ba za ta lamunta ba wajan daukar mataki kamar yadda doka ta tanadar.