Home / News / Ina Goyon Bayan Tsarin Zaben Yartinke (Kato- bayan Kato) Aliyu Waziri

Ina Goyon Bayan Tsarin Zaben Yartinke (Kato- bayan Kato) Aliyu Waziri

Mustapha Imrana Abdullahi
Wani fitaccen dan siyasa da ke fafutukar tabbatar da adalci daga karamar hukumar Kaduna ta Kudu cikin Jihar Kaduna Alhaji Muhammad Aliyu Waziri, da ake wa lakabi da Dan marayan Zaki ya bayyana cewa tsarin zaben Yartinke wato kato bayan kato ne zai yi wa talaka adalci ya zabi abin da yake so.
Muhammadu Aliyu Waziri ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar Talbijin ta DITV da ke Kaduna.
Inda ya ce hakika tsarin zaben fitar da Gwani a tsakanin jam’iyyu na kato bayan kato zai taimakawa dukkan jam’iyyun kasar nan domin kowa zai kasance ya zabi abin da yake bukata domin ya tsayawa Jam’iyyarsa takara.
“Hakika ni ina goyon bayan wannan tsarin domin zai taimakawa al’umma musamman yayan jam’iyya da ke da katin zama yan jam’iyya su zabi abin da suke so, saboda shi zaben wakilai wato “deliget” ya fi sauki wajen fitar da sakamakon zaben fitar da dan takara to amma kuma baya taimakawa jama’a tun daga yayan cikin jam’iyya har zuwa masu gudanar da zaben duk gari baki daya, saboda baya yi wa jama’a kyau shi ya sa kake ganin mutane yan siyasa yau ya na wannan jam’iyya gobe kuma ya canza, misali idan yau ya na APC gobe sai ka ji shi a PDP idan Dare ya yi kuma ya na APGA mai alamar Zakara”, inji Dan marayan Zaki mai sunan siyasa.
“Saboda haka ya na taimakawa ta fuskar rushe jam’iyya ya kuma taimakawa yan takara wajen barin jam’iyya domin idan zaka lura da abin da aka yi a Dimokuradiyyar da aka yi lokacin zaben 2015 in baka misali da mai mulki na yanzu Muhammadu Buhari lokacin da PDP ke yin zaben wakilai su fitar da dan takara, shi tsarinsa Kato- bayan kato ake yi domin wani kudiri ne ya bayar, saboda a sa mutum ya kada kuri’a a siyasance wani aiki ne mai muhimmanci domin ko bai samu nasarar wanda ya zaba ya lashe zabe ba to, ya dai san an bashi yancin yin zaben abin da yake so kuma rashin barin mutane su yi zaben fitar da dan takara na taimakawa wajen Sanya wasu su yi baya baya wajen Jefa kuri’ar babban zabe saboda ta yaya mutum bai yi zaben farko ba sai ace masa ya yi zabe na biyu saboda haka sai kawai ya noke ya ki fitowa kada kuri’ar ma baki daya”.
Waziri Dan marayan Zaki, ya ci gaba da cewa sai ka ji wani ya ce wadanda suka zabi wancan na farko su je su yi zabe na biyu da ake cewa gamagari wato babban zabe, to, amma idan ka zabi naka ni kuma na zabi nawa ba shi kenan ba sai kowa ya zabi abin da yake so idan zaben gari baki daya ya zo.
“Kuma abin da muka fahimta a nan shi ne mafi akasari masu zaben daga deliget din nan idan zaben gari duka yazo ba su fita zabe, don haka ina goyon bayan wannan tsarin da majalisar kasa ta aiwatar na zaben Kato- bayan kato”.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.