Home / Labarai / Ina Jin Cewa Wani Kalubale Ne A Gabana – Sardaunan Danejin Katsina

Ina Jin Cewa Wani Kalubale Ne A Gabana – Sardaunan Danejin Katsina

Ina Jin Cewa Wani Kalubale Ne A Gabana – Sardaunan Danejin Katsina

 

Mustapha Imrana Abdullahi

 

 

Alhaji Sabi’u Sa’idu, shi ne sabon Sardaunan Danejin Katsina Hakimin Mahuta na farko da aka nada a ranar Lahadin da ta gabata a garin Mahuta.

 

Sabon Sardaunan ya bayyana wannan nadin Sarautar Sardaunan Danejin Katsina da aka yi masa a matsayin wani kalubale mai girman gaske a gare shi.

 

 

Sardaunan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ce hakika lokacin da aka gaya masa cewa an bashi wannan Sarautar sai kawai ya tambayi kansa shin me ya yi har aka bashi wannan babbar Sarautar? Kuma zai iya yin abin da mai Sarautar na farko ya yi a lokacin ya na raye? don haka ne nake jin akwai Kalubale a gabana.

“Amma dai na karbi wannan da zuciya daya kuma zan yi dukkan mai yuwuwa inga na sauke nauyi da kalubalen da ke tattare da wannan Sarauta ta Sardaunan Danejin Katsina cikin amincewar Ubangiji.

 

“Hakika wani al’amari ne daga Allah aka ba ni wannan Sarautar ta Sardaunan Danejin Katsina, da aka ba ni wannan takardar cewa an ba ni Sardauna sai na kalli abin matsayin kalubale, amma dai da ikon Allah zan yi abin da mutane ke ganin cewa ina yi domin inganta rayuwar jama’a a koda yaushe, amma ni ina ganin ba wani abu da nake yi duk da haka zan yi kokarin yi wa jama’ar da nake cikinsu aiki sosai domin ci gaba da inganta rayuwarsu”.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.