Home / Ilimi / Sarkin Yaki Bello Kagara Nagari Na Kowa – Dalibai

Sarkin Yaki Bello Kagara Nagari Na Kowa – Dalibai

Sarkin Yaki Bello Kagara Nagari Na Kowa – Dalibai
Mustapha Imrana Abdullahi
Sakamakon irin kokarin da Alhaji Bello Hussaini Kagara yake yi domin ganin an ciyar da ilimi gaba tun daga garin Kagara, Masarautar Danejin Katsina, karamar hukumar Kafur, Jihar Katsina da Nijeriya baki daya ya sa dimbin dalibai daga wannan yankin suka cika garin Kagara su na rera wakoki cewa “Alhaji Bello Kagara Nagari na Kowa”.
Su dai wadannan daliban sun yi jerin Gwano ne a kan titin mashigar garin Kagara a gefe da gefen hanyar shiga garin domin su nuna farin ciki da goyon baya ga sabon Sarkin Yaki na farko a masarautar Danejin Katsina Hakimin Mahuta Alhaji Bello Abdulkadir Yammama, bisa nadin sarautar da ya yi wa dan kishin kasa Alhaji Bello Hussaini Kagara a matsayin Sarkin Yaki na farko a wannan masarauta.
Su dai wadannan yaran sun bayyana cewa Alhaji Bello Kagara ya dade ya na kokarin jawo abubuwan alkairi na ciyar da jama’a gaba, wasu daliban sun ce tun kafin a haifesu duk sun taso su na jin labarin irin yadda Bello Kagara ke kokarin taimakawa harkokin ilimi,addini da kuma dukkan fannonin rayuwa baki daya.
“Amma ga shi mun taso har mun shiga makaranta muna cin gajiyar irin kokarin da Bello Kagara ke yi domin inganta rayuwar al’umma, ya kawo mana makarantu da dama don mu ci gajiyar ilimi kamar yadda ake samu a kowace karkara da birane kuma hakan yake yi tsawon shekaru a dukkan fannonin rayuwa sai dai kawai wanda mutum zai iya tunawa domin ci gaban da ya kawo wa al’umma su na da yawa kwarai”.
Saboda haka nan gaba za mu kawo maku rubutu da sharhi mai yawa a game da wannan bawan Allah.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.